BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ba mu yarda da sakamakon zaɓen Kano da aka kammala ba - NNPP

50260759 Sanata Rabiu Musah Kwankwaso, shugaban jam'iyyar NNPP

Mon, 17 Apr 2023 Source: BBC

Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta ce ba ta gamsu da zabukan ƴan majalisu da aka karasa ba a ranar Asabar 15 ga watan Afurilu.

Jam'iyyar ta ce ba ta yarda da sakamakon ba ne kasancewar tana zargin cewa an tafka magudi a wasu wuraren da aka yi zaben.

Jihar Kano ce ke da ƴan majalisu mafi yawa na jiha wadanda zaɓen su bai kammala ba a zaben 18 ga watan Maris 2023, inda aka kammala zaben a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, kuma aka an sanar da sakamako.

A sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe mazabar dan majalisar wakilai na Tudun Wada da Doguwa, yayin da NNPP kuma ta samu nasara a karamar hukumar Fagge.

Sai zaben ‘yan majalisun dokokin jiha goma sha hudu inda jam'iyyar APC ta samu goma da Gezawa da Tudun Wada da Gwarzo da Makoda da Dambatta da Warawa da Gaya da Dawakin Tofa da kuma Takai da Wudil.

NNPP ta samu kujeru hudu, wadanda suka hada da Ugogo da Gabasawa da Ajingi da kuma Garko.

Sai dai jam'iyyar NNPP, wadda ita ce ta lashe zaben gwamnan jihar ta nuna rashin gamsuwa da yadda zaben ya gudana.

Umar Haruna Doguwa wanda shi ne shugaban jam’iyyar a jihar Kano, ya ce "Akwai abubuwa da dama da suka faru waɗanda ba mu gamsu da su ba, waɗanda kamar an mayar da hannun agogo baya ne."

Ya yi zargin cewa an tayar da hankula a wurare da dama a lokacin zaben da aka kammala.

Ya kuma ce za su yi nazari tare da neman hanyar da za a bi wa ƴaƴan jam'iyyar na NNPP hakkinsu.

Nasarar da na samu ƴar manuniya ce - Ado Doguwa

Zaben majalisar tarayya na karamar hukumar Tudun Wada wanda aka ayyana Alhassan Ado Duguwa a matsayin wanda yayi nasara, shi ne ya fi daukar hankali.

Alhassan Ado Duguwa dai shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai wanda, da wannan nasara, zai sake komawa kan kujerarsa a karo na biyar.

Doguwa ya ce wannan nasara alama ce da ke nuna cewa al'ummar mazabarsa sun amince da wakilcin da yake musu.

An dai soke zaben zaben Ado Doguwa ne wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabarairu, bayan da jami'in bayyana da jami'in hukumar INEC ya ce an tursasa masa bayyana sakamakon duk da cewa akwai rumfuna 19 waɗanda aka soke zaɓukan su saboda tashe-tashen hankali.

Zaben Tudun Wada da Doguwa dai yana daga cikin zabukan da suka zo da sammatsi da tashin hankali al'amarin da yayi sanadin rasa rayuka da kone-kone.

Da wannan dai shi ke nan an kawo karshen zabukan na jihar Kano na 2023, sai dai duk wani ƙorafi game da zaben zai koma gaban kotunan sauraren ƙorafe-ƙorafen zabe inda za su yanke hukunci kan duk wata gardama da ake da ita.

Source: BBC