BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Bankin Duniya ya nuna damuwa kan bashin da China ke bai wa Afirka

David Malpass Shugaban bankin duniya, David Malpass

Mon, 3 Apr 2023 Source: BBC

Shugaban bankin duniya ya faɗa wa BBC cewa ya damu kan rancen da ƙasar China ke bai wa ƙasashen Afirka masu tasowa.

Shugaban bankin, David Malpass ya ce ya kamata sharuɗɗan da ƙasar ke gindayawa su zama waɗanda za a iya cimmawa.

Hakan na zuwa ne bayan damuwa da ake nuna cewa ƙasashe irin Ghana da Zambia na fuskantar matsala wajen biyan Beijing basukan da take bin su.

China ta ce duk wani rance da take bayarwa tana yi ne karkashin dokokin ƙasa da ƙasa.

Ƙasashe masu tasowa na karɓar rance daga wasu ƙasashe ko kuma kungiyoyi domin ciyar da ɓangarorin ƙasashensu musamman ta ɓangaren ababen more rayuwa da ilimi da kuma aikin gona.

Sai dai ƙaruwar kuɗin ruwa kan basukan da Amurka da kuma ƙasashe masu karfin tattalin arziki ke ci gaba da yi a tsawon shekara ɗaya da ta gabata, ya janyo wa ƙasashe matsala wajen biyan basukan saboda an karɓi basukan ne da kuɗin ƙasashen waje kamar dalar Amurka ko yuro.

"Hakan babbar matsala ce kuma yana nufin cewa za a samu tsaiko wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasashe," in ji Malpass.

Hamayya tsakanin Amurka da China

Bukatar shawo kan matsalar da kuma abin da za ta haifar na cikin dalilan da suka sa mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta kai ziyara zuwa wasu ƙasashen Afirka guda uku.

A lokacin ziyarar ce Amurka ta sanar da bai wa ƙasashen Tanzania da Ghana tallafin kuɗi.

Akwai ƙaruwar gogayya da China domin samun tasiri a nahiyar, wadda ke da albarkatun ƙasa irin su ƙarafa da sauran su, waɗanda za a iya sarrafa su ta hanyar fasaha domin ƙera motoci masu aiki da lantarki.

Da take magana a Accra babban birnin ƙasar Ghana, Kamala ta ce "Amurka ba za ta tsaya kan abubuwan da za ta yi wa ƙawayenta ƴan Afirka ba, sai dai da abin da za su yi wa ƙasashen".

Mista Malpass ya yaba wa haɗakar, inda ya ce gogayya tsakanin ƙasashen guda biyu masu karfin tattalin arziki a duniya zai iya zamantowa alkhairi ga ƙasashe masu tasowa.

"Abin da nake ƙara karfafa gwiwa a kai shi ne cewa ƙasashen su kasance masu gaskiya a duk wani rance da za su bayar. Wannan shi ne babbar matsala; idan ka bayar da bashi sannan ka ce kada a nuna wa wani', wannan bai kamata ba."

Shugaban bankin duniyan ya kuma gargaɗi gwamnatoci a Afirka cewa su daina jingine wata kadara a matsayin wadda za su bayar idan suka kasa biyan basukan da suka ciyo.

Ya ce hakan na cutar da al'ummar ƙasashen da ke tasowa, inda ya ce China na cin irin wannan moriya a lokuta da dama.

Beijing ta zama wuri da yawancin ƙasashe masu tasowa ke zuwa domin karɓar bashi a shekarun baya-bayan nan.

Wani sabon bincike da wata cibiya kan kula da tattalin arziki a duniya ta yi, ya nuna cewa China ta bayar da rance da ya kai dala biliyan 185 ga ƙasashe 22 a faɗin duniya tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2021.

China ta musanta cewa tana tatsar wasu ƙasashe da irin basukan da tallafin kuɗi da take ba su.

A wani taron manema labarai a wannan mako, mai magana da yawun mai'aikatar harkokin wajen China Mao Ning, ya ce ƙasar na mutunta bukatar ƙasashe da dama, sannan ba ta taɓa tilasta wa wata ƙasa ba domin ta ciyo bashi, ba ta kuma tilasata su don su biya ba.

Ya ce ƙasar ba za ta sanya wata bukata ta siyasa a cikin yarjejeniyar biyan bashi ba.

Mista Malpass ya ce duk da matsalolin da ake fuskanta wajen ciyo basuka daga China, amma abubuwa na kyautatuwa a yanzu.

"Idan ka duba tarihin basuka da ƙasashen yamma ke bai wa Afirka, wasu lokutan suna bayarwa ne ba domin ƴan ƙasashen su ci gajiya ba. Ko da basukan da Bankin Duniya ke bayar wa, ba a amfani da su yadda ya kamata don moriyar ƴan ƙasa."

"Don haka, abin da muke kokarin yi shi ne, ƙara kyautata yanayin basuka da ake bai wa ƙasashen. Kuma kowa ya kamata ya yi hakan.

"Hanyar da ta kamata a yi hakan ita ce idan akwai wani aiki da za a yi, misali mu ce gina tashar jirgin ƙasa, a duba yadda aikin yake da kuma kuɗin da zai ci. Daga nan sai a san hakikanin kuɗin da zai yi aikin."

Source: BBC