BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Barca ta haɗa maki tara a wasa uku a Champions League

44331550 Yan wasan Barcelona a cikin murna

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Ferran Torres ya ci ƙwallo ya bayar da daya aka zura a raga a wasan da Barcelona ta doke Shakhtar Donetsk 2-1.

Kungiyoyin sun buga wasa na uku-uku a cikin rukuni na takwas a Champions League.

Torres ne ya fara cin kwallo a minti na 28 da take leda, bayan da ya Fermin Lopez ya buga kwallo ta bugi turke sai ta koma ta wajensa shi kuma ya zura a raga.

Daga baya tsohon dan wasan Manchester City, ya bai wa Lopez kwallon da ya zura a raga a minti takwas tsakani.

Shakhtar ta zare daya ta hannun Heorhii Sudakov, bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu a fafatawar.

Barcelona, wadda rabonta da ɗaukar Champions League tun 2015 tana ta daya a kan teburin rukuni na uku da maki tara.

Ita kuwa Shakhtar tana ta uku da tazarar maki shida tsakaninta da ƙungiyar Sifaniya mai rike da kofin La Liga na bara.

Source: BBC