BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Barcelona gidan Messi ne a koda yaushe

Lionel Messi da shugaban Barcelona, Joan Laporta

Mon, 15 May 2023 Source: BBC

Shugaba, Joan Laporta ya ce Barcelona gidan Lionel Messi ne, bayan da kungiyar ke kokarin sake daukar dan wasan a karshen kakar nan.

Kwantiragin kyaftin din Argentina zai kare Paris St Germain a karshen watan Yuni, inda wasu rahotanni ke cewar zai koma Saudi Arabia da taka leda.

Sai dai a wata hira da kafar yada labarai ta Sifaniya TV3, Laporte ya ce za su kalubalancin duk kungiyar da ke son sayen dan wasan mai shekara 35.

Source: BBC