BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Bayanai biyar kan zanga-zangar Iran

68120568 Tutar Iran

Fri, 14 Oct 2022 Source: BBC

An shafe kusan wata guda kenan mutane suna zanga-zanga a Iran, suna kangare wa jami'an tsaro. Ana kallon boren a matsayin wata babbar barazana da ke tunkarar hukumomin Iran a cikin gomman shekaru. Yaya abin ya fara? Abin ya fara ne sakamakon mutuwar Mahsa Amini mai shekara 22 a lokacin da take tsare a hannun ƴan Hisaban Iran, bayan da suka kama ta a Tehran ran 13 ga watan Satumba kan zarginta da keta dokokin ƙasar masu tsauri da ke buƙatar mata su rufe kansu da hijabi ko ɗankwali. Rahotanni sun ce jami'an Hisban sun doke ta da kulke. Amma ƴan sandan Hisabn sun ce ciwon zuciya ne ya yi sanadin mutuwarta. Don tabbatar da hujjarsu, hukumomin sun saki wani bidiyo na Ms Amini a lokacin da ta faɗai a ofishinsu, amma amma bidiyon da hotunan da ke nuna ta a sume - sun ƙara harzuƙa Iraniyawa. An fara yin zanga-zangar farko ne bayan jana'izar Ms Amini a birnin Saddeq da ke yammacin ƙasar, yayin da mata suka yaye mayafansu don nuna zumuncinsu ga marigayiyar. Tun daga sannan zanga-zangar ta girmama, inda masu neman kare ƴanci suke neman a tumɓuke gwamnatin ƙasar. Wace rawa mata ke takawa? Bidiyo sun nuna yadda suka bujirewa ta hanyar ƙona ƴan kwalayensu da yanke gashinsu a bainar al'umma suna ihun cewa "Mata, rayuwa, ƴanci da kuma "Mutuwa a kan mai mulkin kama karya - wata suna nufin Jagoran Addini na ƙasar Ayatollah Ali Khamenei. A yayin da a baya mata ke nuna adawa da hijabi a bainar jama'a, an keɓe wasu an musu hukunci mai tsanani. Sai dai hakan ba komai ba ne idan ak kwatanta da halin da ake ciki. A wani nuna nuna goyon baya da ba a saba gani ba, ƴan mata ƴan makaranta ma suna zanga-zanga a wuraren wasa da kan tituna. Maza da samari ma suna ci gaba da goyon bayan matan a kan buƙatunsu. Me hukumomi ke yi? Hukumomi na ta ƙoƙarin daƙile masu zanga-zangar da ƙoƙarin hana su da ƙarfin tuwo. Ayatollah Khamenei ya zargi Amurka da Isra'ila, manyan abokan gabar Iran, da rura wutar boren - lamarin da masu suka suka yi watsi da shi da cewa ƙarya ne. Mutum nawa aka kashe? An hana BBC da sauran kafafen yaɗa labarai ruwaito abin da ke faruwa daga cikin Iran, lamarin da ya sa da wahala a tabbatar ikirarin kafofin yaɗa labaran ƙasar. Masu fafutuka na shafukan sada zumunta da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun taimaka wajen samar da bayanai, duk da cewa hukumomi sun katse intanet da layukan waya. Ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Iran mai cibiya a Norway, ta ce a ƙalla mutum 201 da suka haɗa da yara 23 ne jami'an tsaro suka kashe. Jami'an tsaron dai sun yi watsi da zargin kisan masu zanga-zangar, amma an ɗauki bidiyonsu suna harbi a kan tituna. Mene ne bambancin zanga-zangar wannan karon da na baya? A shekarar 2009, miliyoyin mutane ne suka bazama kan tituna don nuna adawa ga sakamakon zaɓen shugaban ƙasa mai cike da taƙaddama. Sai dai ba a ko ina aka yi ba sai manyan biranen ƙasar. Matsin tattalin arziki ya uzzura zanga-zangar a 2017 da 2019, amma an yi su a mafi yawancin yankunan da ma'aikata ke zaune. A yanzu kuwa, a karon farko, zanga-zangar ta haɗa da mutane daga kowane rukuni na al'umma da matasa da manya da tsofaffi, ta kuma yaɗu a faɗin gomman birane da garuruwa.

Source: BBC