BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Bayern Munich na sha'awar Kane, Real Madrid za ta sake neman James

24416810 Manchester United ma na son Kane wanda ba ya son barin Premier

Fri, 14 Apr 2023 Source: BBC

Bayern Munich na sha'awar sayen Harry Kane, daga Tottenham a bazara sai da kuma da wuya idan ba Manchester United ce za ta same shi ba saboda kyaftin na Ingila ya fi son ci gaba da zama a gasar Premier. (Mirror)

To amma kuma duk da haka zakarun na Jamus na son jarraba sa'arsu inda za su yi wa Tottenham da dan wasan tayi mai kyau. (Independent)

Liverpool da Chelsea da kuma Manchester United na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Brighton Alexis Mac Allister, dan Argentina, wanda za ta sayar a bazara. (Guardian)

A shirye Real Madrid take ta sake sabon tayi a kan dan bayan Ingila Reece James, idan har an tilasta wa Chelsea sayar da 'yan wasa a bazara. (Mail)

An gayyaci kociyan Bayern Munich Julian Nagelsmann, domin ya gana da hukumar daraktocin Chelsea a kokarin da kungiyar ke yi na neman sabon kociya.

Tuni tsohon kociyan Sifaniya Luis Enrique, ya yi tasa ganawar da shugabannin kungiyar. (Bild)

Barcelona na sa ran ganin Chelsea ta sake yunkurin sayen Raphinha, a bazara. (Sport)

Kylian Mbappe, ya ce burinsa na nan gaba shi ne ya dauki kofin Zakarun Turai da Paris St-Germain, duk da cewa saura kiris ya koma Real Madrid a shekarar da ta gabata. (90min)

Dan gaban Sifaniya Ansu Fati, na son ci gaba da zama a Barcelona, duk da cewa Bayern Munich da Manchester United da Tottenham na sha'awarsa. (Mundo Deportivo)

Manchester City da Chelsea kowacce daga cikinsu ta tura masu yi mata farautar 'yan wasa su je su sa ido a kan dan bayan Monaco Axel Disasi, dan Faransa a karshen makon da ya wuce. (Le Parisien)

Chelsea na da kwarin gwiwar cimma sabuwar yarjejeniya da dan wasanta na tsakiya Mason Mount, na Ingila. (90min)

Fulham na duba yuwuwar zawarcin dan wasan tsakiya na Porto Mateus Uribe, dan Colombia a matsayin wanda zai maye gurbin Joao Palhinha, na Portugal, wanda Manchester United ke so. (Sun)

Dan wasan tsakiya na Colombia James Rodriguez, ba shi da wata kungiya a yanzu bayan da ya cimma yarjejeniyar kawo karshen zamansa a Olympiacos ta Girka. (Liverpool Echo)

Source: BBC