BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Bayern Munich ta kori Oliver Kahn da Salihamidzic

Bayern Munich ta sallami babban jami'inta, Oliver Kahn da daraktan wasanni, Hasan Salihamidzic

Tue, 30 May 2023 Source: BBC

Bayern Munich ta sallami babban jami'inta, Oliver Kahn da daraktan wasanni, Hasan Salihamidzic.

Kungiyar ta sallame su ranar Asabar, bayan lashe Bundesliga na bana, kuma na 11 jimilla.

Bayern ta sallami Kahn, tsohon golanta, wanda ya yi mata wasa 350 da Salihamidzic, wanda ya taka leda tare da Kahn, bayan da ta dauki kofin bana a ranar karshe.

Mataimakin shugaban kungiyar, Jan-Christian Dreesen, shine zai karbi aikin Kahn, yayin da ba a sanar da wanda zai maye gurbin Salihamidzic ba.

Kahn ya shiga cikin mahukuntan Bayern Munich a Janairun 2022 daga nan ya zama babban jami'in kungiyar a cikin watan Yuli.

A karkashinsa Bayern ta lashe Bundesliga biyu da Champions League da European Super Cup da DFB Cup da kuma DFL Supercup.

Tsohon dan kwallon Bayern, wanda ya buga mata tsakiya, Salihamidzic ya zama daraktan wasannin kungiyar a Agustan 2017, daga baya ya shiga cikin manyan mahukuntan kungiyar.

Source: BBC