BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Bellingham ya ci kwallo na 12 a Real da Ingila kawo yanzu

67645808 Jude Bellingham

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Jude Bellingham ya kara ci wa Real Madrid kwallo a wasan da ta doke Sporting Braga 2-1 a Champions League ranar Talata.

Bayan da Rodrygo ya fara zura kwallo a raga tun a zagayen farko, Bellingham ya kara na biyu a minti na 61 da fara karawar, kwallo mai kayatarwa.

Dan wasan tawagar Ingila ya ci kwallo 12 a wasa 15 a Real Madrid da kasarsa tun fara kakar bana.

Alvaro Djalo ne ya zare dayan da Braga ta ci, amma ba ta samu damar farke daya ba, hakan ya sa Real ta ci gaba da jan ragamar rukuni na ukun.

Vinicius Junior ya zaci ya kara na uku a raga, amma alkalin wasa ya kashe ta da cewar ya yi satar gida.

Tun farko Rodrygo ya ci kwallo amma ba a karba ba a zagayen farko da Real ta taka rawar gani da barar da damar maki a Estadio Municipal de Braga.

Da wannan sakamakon, Real Madrid mai Champions League 14 tana jan ragamar rukuni na uku da maki tara a karawa uku.

Yayin da kungiyar Portugal, Braga tana ta uku da maku uku a rukuni na ukun bayyan wasa uku.

Kungiyar Sifaniya ta bai wa ta biyu Napoli tazarar maki uku, wadda ta yi nasara a kan Union Berling 1-0 ranar Talata.

Sakamakon wasannin da aka buga ranar Talata:

Rukunin Farko



  • Galatasaray 1 - 3 Bayern Munich
  • Manchester United 1 - 0 FC Copenhagen


Rukuni na biyu



  • Lens 1 - 1 PSV Eindhoven
  • Sevilla 1 - 1 Arsenal
Rukuni na uku



  • FC Union Berlin 0 - 1 Napoli
  • Sporting Braga 1 - 2 Real Madrid


Rukuni na hudu

  • Inter Milan 2 - 1 FC Red Bull Salzburg
  • Benfica 0 - 1 Real Sociedad


Source: BBC