Tsohon dan wasan Liverpool, Alex Oxlade-Chamberlain (tsakiya)
Tsohon dan wasan Liverpool, Alex Oxlade-Chamberlain ya koma Besiktas kan yarjejeniyar kaka uku.
Mai shekara 29 dan kwallon tawagar Ingila, bai da kwantiragin bayan barin Liverpool a karshen kakar da ta wuce, wanda ya yi shekara bakwai a Anfield.
A lokacin da take sanar da daukar dan kwallon, Besiktas ta ce za ta ke biyansa fam miliyan 2-2 a duk shekara.
Kwantiragin Alexander Mark David Oxlade-Chamberlain ta fara aiki daga ranar 12 ga watan Agustan 2023, za kuma ta karkare a karshen kakar wasan 2025-2026.
Oxlade-Chamberlain ya buga wa Southampton da Arsenal tamaula daga nan ya koma Liverpool a 2017.
Dan wasan da ke buga tsakiya ya yi wa tawagar Ingila karawa 35.
Ya yi fama da jinya dalilin da ya sa baya samun buga wasannin da yawa a Liverpool.