BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Birtaniya za ta haramta wa ɗaliban ƙasashen waje kai iyalansu ƙasar

Hoton alama

Tue, 23 May 2023 Source: BBC

Birtaniya na shirin haramta wa ɗaliban ƙasar waje masu karatun digiri na biyu zuwa da 'yan uwansu ƙasar, a yunƙurin gwamnati na rage yawan 'yan ciranin da ke shiga ƙasar.

An fitar da sanarwar ne kwana biyu kafin alkaluman kididdiga a hukumance da ake sa ran za su nuna cewa waɗanda suka yi hijira zuwa ƙasar sun kai mutum 700,000 a wannan shekara.

A bara, an bai wa mutum 135,788 biza waɗanda ke karkashin kulawar ɗaliban ƙasashen waje, kusan ninki tara a kan adadin da aka bai wa a 2019.

Firaminista Rishi Sunak ya faɗa wa ministoci cewa matakin zai taimaka wajen rage masu ƙaura zuwa ƙasar.

Ya shaida wa majalisar ministocin cewa sauyin da zai fara aiki a watan Janairun 2024, zai taimaka "wajen rage yawan mutane da ke shiga ƙasar," a cewar fadar gwamnatin Birtaniya.

A makon da ya gabata ya ce ministocin suna "la'akari da zaɓin da suke da shi" na rage yawan ƙaura, amma sun ƙi bayyana matakin da aka amince da shi.

A baya dai jam’iyyar Conservative ta yi alkawarin rage yawan mutanen da ke yin ƙaura zuwa Birtaniya zuwa ƙasa da mutum 100,000 a duk, amma ta yi watsi da manufar gabanin zaɓen 2019 bayan da ta ƙasa cimma burin.

Sanarwar ta ce ba za a sake barin ƴan uwa da kuma abokai na ɗalibai masu karatun digiri na biyu su nemi zama a Birtaniya ba yayin karatunsu, sai dai waɗanda ke karatu a kan kwasa-kwasan da aka keɓe a matsayin na bincike.

A shekarar da ta gabata, an bai wa waɗanda ke karkashin kulawar ɗaliban ƙasashen waje 135,788 biza, wanda ya kai sama da kashi biyar na duk bizar da aka bayar na tallafin karatu, idan aka kwatanta da kashi shida a shekara ta 2019.

Sakatariyar Harkokin Cikin Gida Suella Braverman ta ce ba a taɓa samun ƙaruwar mutanen da ke karkashin ɗaliban da ke karatu da ake bai wa biza ba kamar wannan lokaci,” kuma lokaci ya yi da za a ƙara tsaurara hakan wajen ganin an rage yawan bakin haure.

A cikin wata sanarwa da ta aike wa majalisar, ta ƙara da cewa matakin zai "kawo daidaito" tsakanin rage ƙaura da "kare fa'idar tattalin arziki da ɗalibai za su iya kawowa Birtaniya".

Yawan ɗaliban ƙasashen waje a Birtaniya

Kungiyar Jami'o'in Birtaniya mai suna UUK, ta ce ta ga ƙaruwar mutanen da ke karkashin kulawar ɗalibai da ke karatu a ƙasar da ake bai wa biza, wanda hakan ya janyo kalubale kan masaukin iyalai da kuma makaranta.

Shugaban kungiyar UUK ta ƙasa da kasa, Jamie Arrowsmith, ya ce yunkuri da ake yi wajen rage bizar da ake bai wa ƴan uwan ɗalibai abu ne mai kyau.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta haɗa kai da jami’o’i don sanya ido kan tasirin sauye-sauyen, inda ya kara da cewa “za su iya yin tasiri da bai dace ba ga mata da ɗalibai daga wasu ƙasashe”.

A cewar HESA, ƙungiyar bayanai kan ilimi, ta ce akwai ɗalibai 679,970 daga ƙasashen duniya daban-daban a Birtaniya da ke cikin zangon karatu na 2021/2022.

Daga cikin waɗannan alkaluma, ɗalibai 307,470 'yan digiri na farko ne, waɗanda tuni ba za su iya kawo danginsu zuwa Birtaniya ba yayin karatunsu.

Akwai kuma ɗalibai 372, 500 da ke karatun digiri na biyu, inda 46,350 suka kasance masu yin kwasa-kwasan bincike - akasarinsu na neman digirin digirgir ne.

Ɗaliban da ke zuwa Birtaniya tare da biza suna buƙatar samar da takardun da ke tabbatar da dangantakarsu da waɗanda suka dogara, wanda dole ne su biya £490 na kuɗin biza.

Ana kuma buƙatar mutanen da ke karkashin kulawar ɗaliban da su biya ƙarin kuɗin lafiya na hukumar shige da fice - wanda gudummawa ce ta shekara-shekara da ya kai £470 zuwa £624.

Source: BBC