BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Boko Haran sun kashe mutune a Borno, ƴan Bingida na yi wa manoma barazana a Birnin Gwari

Yan yakin Boko Haram

Sun, 2 Jul 2023 Source: BBC

Bayanai na nuna cewa mayakan Boko Haram sun zafafa hare -haren da su ke kai wa wasu yankunan jihar Borno a baya-baya nan.

Rahotannin sun ce akalla mutum biyar ne suka mutu a wani hari da ake zargin mayakan da kai wa kan wani ɓangare na garin Damboa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Mayakan sun kuma jikkata mutane 11.

Sanata Mohammed Ali Ndume shi ne ɗan majalisar dattawa da ke wakiltar yankin, kuma ya shaidawa BBC cewa a daren juma'a ne mayakan suka kai harin in da suka harbo roka daga bayan gari.

"Yanzu an yi jana'izar mutane biyar da suka mutu, kuma 11 da suka ji ciwo, jami'an kungiyar agaji ta Red cross sun taimaka sun kawo helikwafta suka kwashe wadanda aka raunata da ke cikin mawuyacin hali".

Ya kuma ce harin ya rutsa da mata da maza da kuma kananan yara.

Sanatan dai na ganin lura da abubuwan da ke faruwa, akwai bukatar sojojin sama su matsa-kaimi wajen shawagi a yankin.

Ya dangata matsalar hare-haren na Boko Haram a kan dakatar da shawagin jirgin saman soji a yankin

"Rashin sintirin tsaron da ake yi a da, shi yasa 'yan Boko Haran su ke samun dama, su kai hari",In ji shi.

'Birnin gwari na dab da faɗawa cikin yunwa'

A yankin Birnin gwari da ke jihar Kaduna wasu al'ummomi sun ce suna fuskantar barazanar rashin abinci sakamakon yadda 'yan bindiga suka hana su zuwa gonakinsu.

Sun ce 'yan bindigar sun kakaba masu haraji tare da barazanar sace duk manomin da ya tafi gona da kuma cinye amfanin gonaki.

Zubairu Abdulra'uf Idris shi ne Dan Masanin Birnin Gwari kuma ya shaidawa BBC cewa idan ba a dauki mataki ba toh za a yi yunwa a wadannan wurare.

"Har yanzu manoma ba su kai ga gonakinsu ba domin a cikin kashi 100 na manoma kashi talatin ne suka samu suka je gonakinsu.

"Ga shi yanzu watan 7 ake ciki wanda idan nan da makoni biyu ko uku mutane ba su yi shuka ba, toh ina ganin sai dai kawai a hakura da noman".

Ya kuma ce ‘yan bindigar sun bukaci yin sulhu kafin su bari manoma su yi noma a yankin.

"Sun ce tun daga Pandagori zuwa Gidigori ta jihar Neja har Birnin Gwari, ba manomin da zai iya noma, kuma idan ana son manoma su yi noma, to dole sai an yi sulhu da su."

Yankin Birnin Gwari ya dade yana fama da matsalar 'yan bindiga, dasace-sace domin neman kuɗin fansa.

Source: BBC