A Brazil, dubun dubatan mutane sun fito a manya da kananan biranen kasar domi nuna rashin amincewarsu da yadda gwamnatin Shugaba Jair Bolsonaro ke tafiyar da shirin yaki da annobar korona.
A birnin Brasilia, dubban 'yan kasar sun taru a gaban ginin majalisar kasar suna dauke da alluna da aka rubuta bukatunsu da ke cewa shugaban ya sauka daga mulki.
Yadda ta kasance ke nan a gaban ginin majalisar Brazil, inda dubban mutane ke nuna fushinsu kan abin da su ka ce rashin iya aiki da gwamnatin Jair Bolsonaro.
A halin da ake ciki, majalisar kasar Brazil ta na gudanar da wani bincike kan yadda ake tafiyar da aikin yakar annobar korona.
Jerin zanga-zangar da ake yi a birane 200 na kasar za su jaddada wannan matakin na majalisar ne.
Wasu jam'iyyun siyasa da kungiyoyin kwadago na tuhumar Mista Bolsonaro da kin mayar da hankali kan samar da rigakafin cutar ta korona da gangan.
Yawancin masu zanga-zangar na cewa sun gaji da mulkin Mista Bolsonaro, kuma sun bukaci ya ajiye mukaminsa.
kawo yanzu, Fiye da mutum 450,000 sun rasa rayukansu a sanadiyyar annobar Covid-19 a Brazil.