Brazil ta ajiye dan kwallon Manchester United, Antony daga tawagarta, wanda ake zargi da cin zarafin tsohuwar budurwarsa.
Hukumar kwallon kafa Brazil ta ce mai shekara 23 ba zai buga mata karawar ba, bayan da ake zarginsa, wanda za a bincika.
Ranar Litinin wata jarida ta Brazil ta wallafa labarin zargin cin zarafin da Anthony ya yi wa tsohuwar budurwarsa
'Yan sanda a Sao Paulo da na Greater Manchester na bincikar lamarin, yayin da dan kwallon ke musanta zargin.
Ana zargin Antony da farwa tsohuwar budurwarsa, Gabriela Cavallin "wadda ya yi wa gware da ka'' a wani otal a Manchester ranar 15 ga watan Janairu.
Hakan ya sa ta ji ciwo a kanta da ta kai likitoci suka yi mata aiki.
Ta kuma yi zargin cewa ya naushe ta a kirji da ta kai ya yi mata illa da sai da aka yi mata aiki.
Antony ya fada a wata sanarwa cewar alakarsa da tsohuwar budurwarsa sun saba yin hatsaniya, amma bai taba dukanta ko cin zarafinta ba.
Ya taba fitar da wata sanarwa a cikin watan Yuni cewar tsohuwar budurwarsa na yi masa zargin karya na cin zarafi.
Manchester United ta ce babu abin da za ta ce kan batun, bayan da BBC ta bukaci ko za ta yi jawabi kan lamarin.
Wannan batun ya faru ne bayan da kungiyar da take buga Premier League ta sanar da cewar Mason Greenwood zai bar kungiyar, bayan wata shida da aka zarge shi da cin zarafi.
Cikin zargin da aka soke kan Greenwood har da batun fyade da cin zarafi, mai shekara 21 ya koma Getafe ta Sifaniya da zai yi mata wasannin aro.
Brazil ta maye gurbin Antony da dan kwallon Arsenal, Gabriel Jesus a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya da za ta kara da Bolivia da kuma Peru.