BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Brighton ta jefa kociyan Man United cikin matsi

Erik ten Hag, kocin Manchester United

Sun, 17 Sep 2023 Source: BBC

Manchester United ta yi rashin nasara a hannun Brighton 3-1 a wasan mako na biyar a Premier League ranar Asabar.

Minti na 20 da fara wasa ne Brighton ta fara cin kwallo ta hannun Danny Welbeck, na hudu da ya zura a ragar United tsohuwar kungiyarsa.

Shi ne kan gaba a yawan cin United cikin jerin wadanda suka bar kungiyar kuma suka fuskance ta.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Pascal Gross ya ci wa Brighton kwallo na biyu kuma na hudu da ya zura a ragar United a Old Trafford.

A tarihi 'yan wasa biyu ne uka taɓa cin United kwallo biyar a raga a Old Trafford waɗanda suka hada da Steven Gerrard da kuma Mohamed Salah, Gross na dab da shiga cikin wannan jeri.

Saura minti 19 a tasahi daga wasan ne Joao Pedro Junqueira ya ci wa Brighton kwallo, wadda ta hada maki uku a Old Trafford.

To sai dai United ta farke daya ta hannun matashin dan wasa Hannibal Mejbri saura minti 17 a tashi daga karawar.

Karo na biyu a jere Brighton ta ci wasa biyu a jere, bayan cin Newcastle - rabon da ta yi hakan tun Nuwamba zuwa Janairun a bara.

Haka kuma Brighton ta zura kwallo a wasa 16 a jere da ta yi a waje, bajintar da ta taba yi a League 1 tsakanin Agustan 2009 zuwa Fabrairun 2010.

Kafin wasan na ranar Asabar, United ta yi rashin nasara uku a league a hannun Brigton, har da wanda aka doke ta 2-1 a bara a Old Trafford.

United ta ci wasa biyu a gida daga ukun da ta kara a bana kenan, shi ne wanda ta doke Wolverhampton da Nortingham Forest.

Kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama ta yi rashin nasara a gidan Tottenham da Arsenal - za kuma ta ziyarci Bayern Munich a Champions League a makon gobe.

Ita kuwa Brighton wasa daya ta yi rashin nasara a gida a bana, wanda West Ham ta doke ta 3-1 a Premier League.

A makon gobe ne Brighton za ta karbi bakuncin AEK Athens a gasar Zakarun Turai ta Europa League.

Source: BBC