BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Casemiro ba zai buga wa United wasan Newcastle ba

An bai wa Casemiro jan kati a karawar da suka yi da Southampton da suka tashi 0-0 a Old Trafford

Thu, 30 Mar 2023 Source: BBC

Manchester United za ta ziyarci Newcastle United ranar Lahadi, domin buga wasan Premier League mako na 29.

To sai dai Casemiro ba zai yi mata wasan ba, wanda aka dakatar karawa hudu, bayan jan kati da aka yi masa.

An bashi jan kati a wasa da Southampton da suka tashi 0-0 a Old Trafford, inda Anthony Taylor ya kore shi, bayan karbar katin gargadi biyu.

Tun kan nan an kore shi a gasar Premier karo biyu a bana a fafatawa da Crystal Palace ranar 4 ga watan Fabrairu a Old Trafford.

Bai buga wasan da United ta ci Fulham 3-1 a FA Cup ba, ba zai yi fafatawar Premier da Newcastle da Brentford da kuma Everton ba nan gaba.

Akwai karin bayanai.......

Source: BBC