BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Chelsea da Liverpool sun raba maki a Premier League

Chelsea da Liverpool sun tashi 0-0

Tue, 4 Apr 2023 Source: BBC

Chelsea da Liverpool sun tashi 0-0 a kwantan wasan Premier League da suka kara ranar Talata a Stamford Bridge.

Wasan farko da Chelsea ta buga, bayan sallamar Graham Potter ranar Lahadi, bayan da kungiyar ta koma ta 11 a teburin Premier.

Kenan Bruno Saltor ne ya ja ragamar Chelsea a wasan farko a madadin Potter a Stamford Bridge.

Karo na biyar a jere suna raba maki a tsakanin, bayan da suka tashi 0-0 ranar 21 ga watan Janairu a Anfield a karawar farko a bana.

Da wannan sakamakon Chelsea tana mataki na 11 da maki 39, ita kuwa Liverpool ta hada maki 43 tana mataki na takwas a teburin Premier.

Chelsea za ta ziyarci Wolverhampton ranar 8 ga watan Afirilu a wasan gaba a Premier, sannan ta je Real Madrid kwana hudu tsakani.

Real Madrid za ta fara karbar bakuncin Chelsea a wasan farko a quarter finals a Champions League.

Liverpool za ta karbi bakuncin Arsenal a Anfield ranar 9 ga watan Afirilu, mako daya tsakani ta ziyarci Leeds United a Elland Road a Premier League.

Ranar Asabar Aston Villa ta doke Chelsea 2-0 a wasan mako na 29 a Stamford Bride, a ranar Manchester City ta ci Liverpool 4-1 a Etihad.

An fitar da Liverpool a Champions League a kakar nan da FA Cup, sannan ba ta dauki Carabao Cup ba, kenan mataki na hudu take fata a Premier ko ta buga Champions League a badi.

Source: BBC