BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Chelsea da Man United na tattaunawa kan cefenar da Mount

Mason Mount

Fri, 30 Jun 2023 Source: BBC

Ana sa ran a wannan makon za a warware matsalolin da ke tsakanin Chelsea da Manchester United game da sayen Mason Mount.

A makon da ya wuce ne United ta ce ta mika tayin karshe domin sayen dan kwallon na Chelsea.

Chelsea na son a biya ta fan miliyan 58 a kan dan kwallon da kuma wasu 'yan tsarabe-tsarabe.

United na ganin cewa dan wasan ya yi tsada saboda kwantaraginsa na shekara ta karshe a Chelsea.

Chelsea na kokarin rage yawan 'yan kwallonta kuma tuni ta sayar da golanta Edouard Mendy da dan wasan baya Kalidou Koulibaly da kuma Mateo Kovacic.

Shi kuma Kante ya bar Chelsea ya koma Al-Ittihad a yayin da Ruben Loftus-Cheek yake gab da koma wa AC Milan.

Tiemoue Bakayoko shi ma ya bar Chelsea.

Source: BBC