Menu

Chelsea da Saudiyya na neman Mourinho, PSG za ta rabu da Messi da Neymar

Jose Mourinho

Fri, 7 Apr 2023 Source: BBC

Chelsea ta tuntubi tsohon kociyanta kuma na Roma a yanzu Jose Mourinho domin ya sake komawa kungiyar ta Stamford Bridge a karo na uku. (Relevo)

Haka kuma Mourinhon ya samu tayin tafiya Saudiyya aiki na shekara biyu inda za a ba shi albashin yuro miliyan 120. (Corriere dello Sport )

Har-wa-yau Chelsean na neman sayen dan gaban Benfica Goncalo Ramos, dan Portugal mai shekara 21. (Football Insider)

Inter Milan na son kulla wata sabuwar yarjejeniya da dan bayanta na Italiya Alessandro Bastoni, yayin da Manchester City ke nuna sha'awarta a kan dan wasan mai shekara 23. (Calciomercato)

Barcelona na da kwarin gwiwa cewa za ta iya sayen dan bayan Portugal Joao Cancelo daga Manchester City a bazara. A yanzu dan wasan mai shekara 28 yana zaman aro ne a Bayern Munich. (Sport)

Manchester United na tattaunawa tsawon makonni a kan cinikin Jeremie Frimpong na Bayer Leverkusen, wadda ke son a ba ta yuro miliyan 50 a kan dan bayan mai shekara 22. (Bild )

Barcelona da Bayern Munich su ma suna son matashin dan wasan na Holland a bazara mai zuwa. (Fabrizio Romano)

AC Milan ta cimma sabuwar yarjejeniya da Rafael Leao, dan gaban Portugal mai shekara 23.(Relevo)

Kylian Mbappe, ya bayyana sosai a wani hoton bidiyo na tallata tikitin kallon wasannin kaka ta gaba ta 2023-24 na PSG, amma kuma ba maganar Lionel Messi, ko Neymar a bidiyon. (Le Parisien)

Dan wasan tsakiya na Austria Marcel Sabitzer, na shawara kan ko ya ci gaba da zaman dindindin a Manchester United, wadda ta karbo aronshi daga Bayern Munich. (Sky Sport)

Arsenal na kara azama ta ganin ta sayi dan wasan tsakiya na Switzerland Djibril Sow, mai shekara 26, daga Eintracht Frankfurt a bazara. (Mirror)

Newcastle na sha'awar sayen dan gaba na gefe na West Ham Jarrod Bowen, dan Ingila. (Talksport)

Leeds United na son saye dan wasan tsakiya da ta dauko aro daga Juventus Weston McKennie, dan Amurka idan har ta tsira daga faduwa daga Premier. (Calciomercato)

Kungiyar Altay SK ta Turkiyya ta ce Manchester City da Atletico Madrid da Sevilla sun tuntube ta domin ta sayar musu da matashin dan bayanta Efe Sarikaya, dan Turkiyya mai shekara 17. (Sport)

Leeds United ta sha gaban Everton a zawarcin dan gaban Coventry City Viktor Gyokeres, na Sweden. (Football Insider)

Edinson Cavani wanda a yanzu yake taka leda a Valencia ya ce ba har yanzu ba shi da tunanin yin ritaya duk da ya kai shekara 36. (AS )

Tottenham ta dauki gwajin matashin dan bayan Kilmarnock Ben Brannan, dan Scotland mai shekara 16, kafin ta saye shi idan ya yi mata daidai. (Football Insider)

Source: BBC