A farkon watan Agusta abubuwa suka fara dagule wa magoya bayan Chelsea.
A lokacin, Chelsea na dab da buga wasanta na ƙarshe a wasanni da ake yi gabanin fara kaka a zagayen da suka je Amurka, inda za su fafata da Borussia Dortmund yayin da suke jin za su fara shiga wani sabon yanayi.
Sabon koci, sabbin 'yan wasa' ga sabon mai zuba kuɗi a ƙungiya. Komai sabo.
Suna jin cin fuskar da suka fuskanta a kakar da ta wuce da suka kammala a mataki na 12 za ta zo ƙarshe duk da cewa abin da ciwo.
Mai yi wa BBC sharhi Alex Howell ya zaɓi ‘yan wasa biyu da yake tsammanin tauraruwarsu za ta haska, waɗanda suka hada da Christopher Nkunku da Nicolas Jackson.
Nkunku ya ci kwallo uku cikin wasa biyar da ya buga – duka ya ci su ne a matsayin ɗan wasan gaba da ke bi ta tsakiya – ya nuna kwarewa da gogewa a wajen cin kwallo.
Kwatsam, sai ga tsautsayi.
Dan ƙasar Faransan ya ji rauni a gwiwarsa, abin da ya sa har yanzu bai buga mata ko wasa guda ba kenan. A rashinsa, Chelsea na matsayin da ta gama kakar bara - na 12.
Yanzu da yake shirin dawowa, ana tsammanin nasarar ƙungiyar za ta dawo.
Ya ci ƙwallo 58 a kaka biyu da ya buga a RB Leipzig, wani abu da ake ta tsammanin ci gabansa a Chelsea.
Tun a watan Oktoban 2022 aka cimma yarjejeniya tsakanin Chelsea da ɗan wasan, amma ana sa ran dawowarsa za ta zama waraka ga ƙungiyar, wani ɗan wasa da ta ɗauka da ake yi wa kallon mafi muhimmanci a wannan kakar.