BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Chelsea ta dauko dan Ivory Coast David Datro Fofana

99287291 Dan kwallon Ivory Coast David Datro Fofana

Fri, 30 Dec 2022 Source: BBC

Chelsea ta sanar da kulla yarjejeniya da dan kwallon Ivory Coast David Datro Fofana daga kungiyar Molde FK ta Norway.

Fofana mai shekaru 20 da haihuwa, ya ci kwallo 15 a wasanni 24 da ya buga gasar kwallon Norway.

Chelsea na karancin 'yan wasan gaba, bayan Armando Broja ya ji rauni kuma zai yi jinyar lokaci mai tsawo.

"Chelsea ta kammala yarjejeniya da Molde FK game da sayen David Datro Fofana. Zai hade da mu a ranar 1 ga watan Janairu," in ji Sanarwar da Chelsea ta fitar.

Dan wasan na Ivory Coast ya soma buga wa kasarsa kwallo yana da shekaru 17 a wasan da suka buga da Nijar a shekara ta 2019.

Source: BBC