Chelsea ta kusan kammala sayen dan kwallon Faransa, Lesley Ugochukwu daga Rennes kan fam miliyan 23.2.
Ugochukwu, mai shekara 19, ya buga wa Rennes wasa 47 a Ligue 1, ya kuma fafata a Europa League.
Har yanzu bai yi babbar tawagar tamaula ta Faransa wasa ba, amma ya taka leda a matasan Faransa 'yan kasa da shekara 17 da 'yan 18 da kuma 'yan 19.
A baya sabon kociyan Chelsea, Mauricio Pochettino ya sanar cewar suna bukatar wani dan kwallon mai wasa daga tsakiya.
Chelsea na sayen matasan 'yan kwallo, wadanda za ta mora a nan gaba, yayin da take kokarin sayar da wasu, bayan kashe fam miliyan 600 wajen sayo 'yan kwallo a kakar da ta wuce.
Tuni kungiyar ta sayar da Kai Havertz ga Arsenal da Mateo Kovacic ga Manchester City da kuma Mason Mount ga Manchester United a bana.
Yayin da 'yan wasa da suka hada da N'Golo Kante da Kalidou Koulibaly da Edouard Mendy suka koma buga gasar tamaula ta Saudi Arabia.
Ruben Loftus-Cheek da kuma Christian Pulisic sun koma buga gasar Serie A tare da AC Milan.
Chelsea na son sayen dan wasan Brighton, Moises Caicedo, wanda ta taya karo uku amma an ki sallama mata shi.
Tuni Chelsea ta dauki 'yan wasa masu buga gurbin masu cin kwallo a bana da suka hada da Christopher Nkunku da Nicolas Jackson da kuma matashi, Angelo Gabriel.