BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Chelsea ta sayi Gusto daga Lyon

Malo Gusto

Sun, 29 Jan 2023 Source: BBC

Chelsea ta saye mai tsaron bayan Lyon da Faransa, Malo Gusto kan fam miliyan 31.

Gusto ya zama dan wasan Chelsea daga nan har zuwa 2030, amma kuma zai cigaba da zama Lyon ne har zuwa karshen kakar da ake ciki.

Matashin ya fara wasa a kungiyar tasa ne daga matakin kasa, har ya samu gurbi a babban mataki.

Ya buga wa Lyon wasa sau 15 a bana, kuma a yanzu yana mataki na tara a gasar Ligue 1.

Gusto ya shiga sahun sabbin yan wasan da Chelsea ta siyo, da suka hada da Madueke, Mudryk, Santos, Fofana, Badiashile da kuma Felix.

Source: BBC