BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Chelsea za ta ƙara kuɗi kan Moises Caicedo, Newscastle na shirin sayar da Allan Saint-Maximin

Moises Caicedo

Fri, 21 Jul 2023 Source: BBC

Chelsea na duba yiwuwar kara kuɗi zuwa fam miliyan 80 a kan ɗan tsakiyar Brighton Moises Caicedo, mai shekaru 21. (Mail)

Kazalika Chelsea na kuma duba yiwuwar dawo da Marc Guehi, mai shekaru 23 da ta sayar shekaru biyu da suka gabata ga kungiyar Crystal Palace. (Guardian)

Manchester City na harin dan wasan gefen Barcelona dan kasar Brazil Raphinha, mai shekaru 26, wanda ta ke son ya maye gurbin dan wasan Algeria Riyad Mahrez mai shekaru 32 da zai koma Al-Ahli. (Foot Mercato - in French)

Newcastle na shirin sayar da dan gefen Faransa Allan Saint-Maximin, mai shekaru 26 ga kungiyar Al-Ahli kan kudi kusan fam miliyan 30. (Telegraph - subscription required)

Al-Nassr ta kara farashi kan tayin da ta yi wa dan wasan Bayer Leverkusen Moussa Diaby, yayin da Aston Villa kuma tuni ta miƙa tayinta ga dan gefen Faransan mai shekaru 24. (Fabrizio Romano)

Tottenham na duba yiwuwar dauko dan gaban Brazil Pedro mai shekaru 26, wanda ke yi wa Flamengo wasa. . (Independent)

Tayin fam miliyan 15 zai iya ba iwa Bournemouth dama ta wuce Borussia Dortmund, da Barcelona da kuma Real Madrid wajen daukar dan wasan Spaniya Ivan Fresneda mai shekaru 18, daga Real Valladolid a kakar bana. . (Football Insider)

Atletico Madrid ta bai wa dan wasan Portugal Joao Felix, mai shekaru 23, dama na cika burinsa na komawa Barcelona da buga wasa. . (AS - in Spanish)

Atletico ta kuma tuntubi Paris St-Germain kan Marco Verratti, to amma har yanzu ba ta bayyana kudin da za ta bayar ba kan dan wasan tsakiyar na Italiya. (L'Equipe - in French)

Arsenal na bibiyar dan tsakiyar Dinamo Zagreb Martin Baturina, mai shekaru 20, wanda ya taka rawar gani a gasar kasashen nahiyar Turai ta ‘yan ƙasa da shekara 21. . (Express)

Source: BBC