Kociyan Chelsea, Mauricio Pochettino ya ce suna ta kokarin daukar wani dan wasa mai cin kwallaye, bayan da Christopher Nkunku zai yi jinya mai tsawo.
Dan wasan tawagar Faransa, mai shekara 25, zai yi jinya mai tsawo, bayan da ya ji rauni a lokacin da kungiyar ke atisayen tunkarar kakar bana a Amurka.
Nkunku ya ji rauni a gwiwar kafarsa a wasan sada zumunta da Borussia Dortmund a Chicago.
Nkunku, wanda ya koma Chelsea kan fam miliyan 52 daga RB Leipzig a bana, ya taka rawar gani a wasa biyar da ya yi wa Chelsea da cin kwallo biyar.
''Muna tausaya masa. Yana taka rawar gani, yana da matukar amfani a tare da mu.''
Chelsea za ta fara wasan farko a Premier League ranar Lahadi da karbar bakuncin Liverpool.
Chelsea za ta tunkari kakar bana tare da sabon kociya, Mauricio Pochettino.
'Yan wasa da yawa sun bar Chelsea a bana da suka hada da Kai Havertz da N'Golo Kante da Kalidou Koulibaly, da Mateo Kovacic da Edouard Mendy da Mason Mount da kuma Christian Pulisic.
Chelsea, wadda ta kare a mataki na 12 a teburin Premier League ta dauki Nicolas Jackson da Lesley Ugochukwu da Angelo Gabriel da Diego Moreira da Robert Sanchez da kuma Axel Disasi.