BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

China ta musanta zargin tallafa wa ayyukan ta'addanci a Najeriya

Hoton alama

Wed, 19 Apr 2023 Source: BBC

Gwamnatin China ta musanta zargin cewa tana biyan 'yan ta-da-ƙayar-baya cin hanci don samun damar shiga wuraren ayyukan haƙar ma'adanai a Najeriya.

China ta ce ba za ta taɓa sa hannu a cikin duk wani abu da ya danganci tallafa wa ayyukan ta’addanci ba.

Martanin na zuwa ne bayan wani rahoto da jaridar Times ta Burtaniya ta wallafa ranar 15 ga watan Afrilu, da ke cewa "Beijing na tallafa wa ayyukan ta’addanci a kaikaice" a Najeriya.

Wani bincike da ƙungiyar bin diddigin al'amura ta SBM da ke birnin Lagos ta aika wa jaridar Times ya nuna wasu hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta irin na WhatsApp na wasu shugabannin 'yan ta-da-ƙayar-baya suna bugun ƙirjin cewa suna da ƙarfin da dole duk wasu ma’aikatan China da ke son fara aikin haƙar ma'adanai a yankunansu, sai sun biya su harajin ƙasa.

Sai dai wata sanarwa da ofishin jakadancin China a Najeriya ya fitar ta bayyana rahoton a matsayin ‘’maras kan gado’’ inda ya kuma nuna rashin jin daɗin gwamnatin ƙasar kan wannan rahoto.

"Zarge-zargen da ke ƙunshe a rahoton", in ji sanarwar ofishin jakadancin China ba su da wani tushe balle makama, kuma akwai ayar tambaya game da rahoton".

"Gwamnatin China da ma ofishin jakadancin China a Najeriya ko da yaushe suna ƙarfafa gwiwa tare da yin kira ga kamfanonin China da ‘yan ƙasar da ke zaune a Najeriya su kasance masu bin doka da oda".

Jaridar HumanAngle ta intanet a Najeriya ita ma ta ba da rahoton cewa masu aikin haƙar ma’adinai a yankin arewa maso yammacin Najeriya suna biyan 'yan fashin daji harajin kashi 10% na abin da suke samu duk wata.

Manufar hakan ita ce su samu amincewa don ci gaba da ayyukansu na haƙar ma’adinai.

Ofishin jakadancin China a Najeriya dai ya jaddada cewa a tsawon shekaru da dama, dangantaka tsakanin China da Najeriya ta taimaka wajen bunƙasa ci gaba mai amfani ga duk ƙasashen biyu da ma al’ummominsu.

"Don haka za mu ci gaba da aiki da gwamnatin Najeriya don tabbatar da ci gaban ƙasar da shawo kan matsalolin tsaro.

Muna kuma maraba da abokan hulɗa na duniya, su shigo cikin wannan yunƙuri amma za mu yi watsi da duk wata aniya ko matakin da zai gurbata alaƙarmu," in ji sanarwar.

Source: BBC