BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Cinikin Rice ya fada, Man Utd na zawarcin Caicedo da wasu

Declan Rice

Fri, 30 Jun 2023 Source: BBC

An bai wa dan wasan tsakiya na Ingila na West Ham Declan Rice, damar ya je a gwada lafiyarsa a Arsenal, yayin da kungiyoyin biyu ke tattaunawa yadda za a kasa kudin cinikinsa fam miliyan 105. (Talksport)

Shi kuwa kociyan West Ham David Moyes yana harin dan wasan tsakiya na Everton Amadou Onana, dan Belgium mai shekara 21, da dan wasan tsakiya na Juventus Denis Zakaria, dan Switzerland mai shekara 26, da kuma dan bayan Manchester United Harry Maguire. (Mirror)

A shirye Bayern Munich take ta bayar da fam miliyan 80 domin a sayar mata da Harry Kane, bayan da Tottenham ta ki yarda da tayin fam miliyan 60.2 da kungiyar ta Jamus ta fara yi a kan kyaftin din na Ingila. (Sun)

Man Utd za ta gabatar da bukatarta ta sayen dan wasan tsakiya na Brighton Moises Caicedo, dan Ecuador mai shekara 21, bayan da ta fara tuntuba a makon nan. (Sky Sports)

Haka kuma Red Devils din za su tattauna da Chelsea a makon nan domin kawar da matsalar da ta sa suka kakare a kan batun cinikin Mason Mount. (Telegraph )

Dan wasan tsakiya na Sifaniya Gabri Veiga, wanda kwantiraginsa da Celta Vigo ya tanadi sayar da shi a kan yuro miliyan 40 ga duk mai so, ya kasance wanda Manchester City, ke nema a yanzu, yayin da Liverpool da Chelsea su ma suke son matashin mai shekara 21. (Fabrizio Romano)

Liverpool ta gana da wakilan matashin dan wasan tsakiya na Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekara 22, wanda tsayayyen farashinsa a kwantiragin RB Leipzig shi ne yuro miliyan 70. (Athletic)

Wolves ta amince da tayin fam miliyan 7.5 tare da wasu tsarabe-tsarabe na karin fam miliyan 1 daga Leicester a kan dan bayan Ingila Conor Coady. (Express and Star)

Burnley ta mika tayinta na sayen matashin dan bayan Anderlecht Noah Sadiki dan Belgium mai shekara 18. (Fabrizio Romano)

A shirye Chelsea take ta sayar da dan wasanta na gaba na gefe Callum Hudson-Odoi na Ingila a kan fam miliyna 15, kuma Nottingham Forest na sha'awarsa. (Nottingham Post)

Gwanin matashin dan wasan Santos Angelo, mai shekara 18, wanda ya yi wa Brazil wasa a tawagar 'yan kasa da shekara 20 na daf da kammala tafiyarsa Chelsea a kan yuro miliyan 15, bayan da Barcelona ta janye daga zawarcinsa. (GOAL)

Leeds na sha'awar sayen dan bayan Liverpool Nat Phillips, na Ingila (Athletic)

Shugaban Benfica Rui Costa ya ce Man Utd ta shirya biyanyuro miliyan 80 a kan dan gaban kungiyar Goncalo Ramos dan Portugal. (Correio da Manha, ta FourFourTwo)

Source: BBC