Real Madrid za ta fafata da Al Ahly a daf da karshe a Club World Cup ranar 8 ga watan Fabrairu da Morocco ke karbar bakunci.
Ranar Asabar kungiyar Masar ta yi nasara a kan Seattle Sounders da ci 1-0, kuma Mohamed Afsha ne ya ci kwallon saura minti biyu a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon Al Ahly, wadda Marcel Koller ke jan ragama za ta fuskanci Real Madrid ranar Laraba a Rabat.
Ita kuwa kungiyar Saudi Arabia, Al Hilal ta yi nasara a kan Wydad Casablanca ta Morocco a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 ranar Asabar 4 ga watan Fabrairu.
Al Hilal ta kai daf da karshe kenan da cin 5-3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Da wannan sakamakon Al Hilal za ta fuskanci Flamengo a daya wasan daf da karshe ranar Talata 7 ga watan Fabrairu.
Ranar 11 ga watan Fabrairu za a buga neman mataki na uku tsakanin wadda aka doke ranar Talata da wadda ta yi rashin nasara ranar Laraba.
A dai ranar ta Asabar 11 ga watan Fabrairu za a buga wasan karshe a filin Moulay Abdallah tsakanin wadda ta yi nasara ranar Talata da Laraba.