Wannan shafi ne da yake kawo muku bayanan adadin masu kamuwa da cutar korona kullum a Najeriya, daga bayanan hukumar NCDC. Muna sabunta shi ne da zarar an samu sabbin bayanai kullum.
Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 464 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Laraba.
Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 131 da aka tabbatar sun kamu da cutar.
Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 69 a jihar Kaduna da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.
Mutum 33 kuma sun kamu da korona a Akwa Ibom sai Imo mai mutum 31, da jihar Katsina da aka gano mutane 30 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.
A Kano an gano mutane 26 da suka kamu da cutar korona ranar ta Laraba.
Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi
■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.