Cristiano Ronaldo ya ce burinsa ya cika tun daga lokacin da ya koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus a 2018.
Kyaftin din tawagar Portugal ya ce ya ji dadi da matsayin da kungiyar ta kai a bana duk da cewa ta kasa lashe Serie A, bayan tara a jere da ta lashe a baya.
Sauran kwantiragin kaka daya ta rage wa Ronaldo, mai shekara 36 a Juventus, sai dai ana ta rade-radin cewar zai bar kungiyar a karshen kakar bana.
Inter Milan ce ta lashe kofin Serie A na bana yayin da Juventus ta samu gurbi na hudu a ranar karshe ranar Lahadi, bayan da ta je ta yi nasara a kan Bologna da ci 4-1.
"Wannan kakar ba mu dauki Serie A ba, muna taya Inter Milan murna kan kokarin da suka yi, ina murna da rawar da muka taka da nasarorin da kungiyar ta samu da ni kaina", kamar yadda Ronaldo ya rubuta a Instagram.
Ya ce: "Lashe Italian Super Cup da Italian Cup da zama wanda ke kan gaba a cin kwallaye a Italiya ya sanya ni cikin murna, musamman saboda kalubalen da muka fuskanta a kasar da komai baya zuwa cikin sauki.
"Wadannan nasarori na nufin cewa na cimma burin da na sa a raina tun farkon da na koma taka leda a Italiya - cin Serie A da Italian Cup da Super Cup da zama fitaccen dan wasa da wanda ya lashe kyautar yawan zura kwallaye a raga a babbar kasar tamaula da kwararrun 'yan wasanmu a babbar kungiyar, haklika na cika burina.''
Ronaldo, mai shekara 36, tsohon dan kwallon Manchester United da Real Madrid ne kuma ya kara da cewar yana cike da farin ciki da ya lashe manyan gasa a kungiya uku daga kasashe uku.
Ronaldo zai ja ragamar tawagar kwallon kafar Portugal gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana da za a fara cikin watan Yuni a kammala a Yulin 2021.