Menu

'Da an ga baƙar fata sai a ce wannan ba ɗan Tunisiya ba ne'

Khawla Ksiksi ta ce wani lokacin tana jin cewa kamar da gaske ba 'yar Tunisiya ba ce

Mon, 12 Jun 2023 Source: BBC

Baƙaken fata a Tunisiya sun bayyana cewa suna fuskantar ƙarin wariyar launin fata tun bayan da shugaban ƙasar ya soki 'yan ƙasashen baƙar fata na Afirka.

"A Tunisiya kodayaushe mutane sai su dinga nuna shakkun kasancewata 'yar Tunisiya," a cewar wata mai fafutika Khawla Ksiksi, 'yar Tunisiya.

A watan Fabarairu Shugaba Kais Saied ya ba da umarnin ɗaukar matakai kan baƙaƙen fata daga da suka je cirani daga ƙasashen baƙr fatar Afirka bayan ya zarge su da yunƙurin "shirya maƙarƙashiyar" ƙara yawan al'umma da kuma al'adun ƙasar.

Ya ƙara da cewa ana zuwa ƙaura ƙasar ne "da zimmar mayar da Tunisiya wata ƙasar Afirka a madadin ƙasar Larabawa kuma Musulmai".

Tuni aka fara samun ƙaruwar hare-hare kan baƙaƙen fata 'yan cirani, kamar yadda ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rights Watch ta bayyana.

Baƙaƙen fata a Tunisiya sun kai kashi 10 zuwa 15 na al'ummar ƙasar, kamar yadda alƙaluman hukumomi suka nuna.

Cikin wannan adadi akwai waɗanda dangin bayi ne - an haramta cinikin bayi a Tunisiya kusan shekara 180 da suka wuce - yayin da wasu kuma suke da asali fiye da haka.

Ms Ksiksi ta faɗa wa BBC cewa lamarin ya sa tana jin kamar ba ta raye: "Wani lokacin idan na yi magana da Larabci sai su amsa da Faransanci saboda ba sa so na zama wani ɓangare na Tunisiya."

Larabci ne harshen hukuma a Tunisiya. Duk da cewa ana kallon Faransanci a matsayin harshen masu kuɗi da ilimi, harshe ne na "baƙi", saboda haka duk lokacin da wasu suka amsa mata da Faransanci suna nufin ba sa ɗaukar ta a matsayin 'yar Tunisiya.

Ms Ksiksi wadda ita ce shugabar ƙungiyar kare haƙƙin matan Tunisiya ta Voices of Black Tunisian Women Collective, ta ƙudiri aniyar yaƙar tunanin cewa babu baƙaƙen 'yan asalin ƙasar.

"Ina jin cewa ni 'yar Tunisiya ce duk da cewa ana nuna min wariya [da kuma baƙaƙen fata irina]," a cewar 'yar shekara 31 ɗin.

"Ba sa mu'amalantarmu a matsayin 'yan Tunisiya kuma suna kallonsu su ba 'yan Afirka ba ne."

Ta ce duk da samun 'yancin kai daga Faransa a 1956, 'yan Tunisiya na son a dinga kallon su a matsayin Turawa, sannan kuma baƙaƙen fatar Tunisiya "ƙazamai ne" da suka share wuri suka zauna.

"Dalilin da ya sa ke nan muke da babbar matsalar al'adu a Tunisiya. Mun samu 'yanci a rubuce, amma har yanzu siyasar mulkin mallaka na nan."

Tana ganin ƙrancin wakilci da baƙaƙen fata ke da shi a fagen siyasa da kuma gwamnati na ƙara rura wutar tunanin babu baƙaƙen fata 'yan Tunisiya.

"Baƙar fatata na nuna cewa ni ba 'yar ƙasa ba ce, saboda haka mu baƙaƙen Tunisiya so ake yi kullum mu yi ta nuna cewa mun kai," in ji Ms Ms Ksiksi.

Lamarin ya fin ƙamari a kan mata baƙaƙe, a cewarta: "A makaranta, dole ne na dinga cin maki mai yawa a kodayaushe saboda dukkan malaman na ganin satar amsa nake yi, don a tunaninsu baƙar fata ba shi da hazaƙa."

'Yar gwagwarmayar ta ce tana da arzikin da za ta iya samun ilimi mai kyau sosai, amma kuma hakan yakan sa ta ware kanta: "Ganin cewa ke kaɗai ce baƙar fata a aji sai ki ji duk kin zama ke kaɗai kuma babu mai taimaka maki.

"Sai na dinga jin cewa komai fari ne amma ni kaɗai ce baƙi a cikinsu."

Kamar Ms Ksiksi, ita ma Houda Mzioudet ta ce matsalar da ake fuskanta ita ce an gina Tunisiya a kan wani "tsarin kishin ƙasa na bai ɗaya" wanda bai ba da damar tayar da batun wariyar launin fata ba.

"Abin da ya fi ciwo ma a Tunisiya ba wariyar launin fatar ba ce, musanta batun wariyar ne, inda za a dinga tsangwamar ki kan laifin wariyar da aka yi maki," a cewar 'yar shekara 46 ɗin, wadda malamar jami'a ce kuma mai bincike.

A matsayin martani ga kalaman shugaban ƙasar, wasu daga mata baƙaƙen fata, ciki har da Ms Mzioudet, sun shiga gangamin "Carrying My Papers Just In Case" a Facebook - wato "Yawo da Takarduna Saboda Tsautsayi".

Suka dinga rataya fasfo ɗinsu da katinan shaida a jikinsu don su nuna cewa su 'yan Tunisiya ne amma kuma suna goyon bayan 'yan cirani.

A wajen MS Mzioudet, kalaman shugaban ƙasar kan baƙaƙen fata 'yan cirani martani ne da ya biyo bayan zanga-zangar ƙasashen Larabawa.

A 2011, shugaban da ya fi daɗewa a mulkin ƙasar, Zine al-Abidine Ben, ya gudu daga ƙasar sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke. Ƙirƙirar tsarin dimokuraɗiyya da aka yi daga baya ya bai wa baƙaƙen fata damar fitowa bainar jama'a a ƙasar.

Daga baya baƙaƙ sun ci gaba da neman ƙarin wasu haƙƙoƙi na daidaito, kuma Ms Mzioudet ta fi jin daɗi idan tana siffanta kanta a matsayin baƙar fata.

A 2018, Tunisiya ta amince da wata doka mai muhimmanci da ke haramta wariyar launin fata, nuna wa baƙaƙen fatar ƙasar da 'yan cirani wariya a taƙaice.

Ita ce ƙasar Larabawa ta farko da ta saka irin wannan doka da ta ayyana aikata wariyar launin a matsayin laifi.

Ms Ksiksi da Ms Mzioudet sun ce duk da waɗannan dokoki gwamnati ta bari ana ci gaba da nuna wa baƙaƙen fata wariya.

A watan Fabarairu, ɗaruruwan mutane suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga baƙaƙen fata 'yan cirani, abin da ke nuna alamar akwai yiwuwar matasan ƙasar za su buƙaci sauyi, a cewar Ms Mzioudet.

"Sai da na zubar da hawaye lokacin da na ga macin da aka yi a birnin Tunis wanda ya ƙunshi akasari fararen fatar Tunisiya, waɗanda ke cewa rayuwar baƙaƙe na da daraja," in ji ta.

"Kuma ba wai magana ce ta baƙaƙen fata ba, haƙƙin ɗan Adam ne."

Source: BBC