Yayin da yaƙi tsakanin Hamas da Isra'ila ke tsananta, an riƙa aza ayar tambaya kan ƙasashe ko ƙungiyoyin da ke ɗaukar nauyin Hamas, kuma daga ina wannan ƙungiya ke samun kuɗaɗe?
Bayan tunanin wanda ya ƙarfafa ƙungiyar da har ta kwashe kusan shekara 20 tana iko da Gaza?
Shekara biyu da suka gabata, a yaƙinta na ƙarshe da Isra'la da ya ƙare cikin kwana 11, Hamas harba rokoki 4,000.
Amma a wannan shekara, a harin 7 ga watan Oktoba, ta harba dubban rokoki a cikin kwana guda kacal.
Wannan ya nuna cewa ƙungiyar na da tarin makaman roka.
Baya ga ɗaukar nauyin soji, yana da matuƙar muhimmanci mu bayyana albashin ma'aikatanta kusan 50,000 da ke Zirin Gaza, wanda ƙungiyar ta ce tana kashe fiye da dala miliyan 30 a kowanne wata
Baya ga wannan, Hamas kan taimaka wa mutanen da suka rasa iyalansu, ko mutanen da suka jikkata a wasu yaƙe-yaƙe.
Haka kuma Hamas na biyan kuɗin wuta da na lantarki da kudin hayar gidaje ga mutanenta.
Ƙasashen da ke taimaka wa Hamas
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce kasafin kuɗin gwamnatin Gaza ya zarta dala miliyan 700 a kowace shekara, inda aka ware dala 260 kan ayyukan yau- da-kullum.
Tallafin kuɗi ga Hamas da kuma gwamnatin Zirin Gaza na samuwa ta hanyoyi daban-daban.
Sukan samu tallafin kuɗi daga wasu gwamnatocin ƙasashen duniya. Sukan samu tallafi daga ɗaiɗaikun 'yan ƙasa da ƙungiyoyin tallafi.
Sukan samu wasu kuɗi ta hanyar aiki a kamfanonin kasuwannin kirifto, sukan kuma samu kuɗi daga zuba jri a wasu ƙasashe.
An ce Iran, da Qatar da Kuwait da Turkiyya da Saudiyya da Algeriya da Sudan da Hadaɗdiyar daular Larabawa na daga cikin ƙasashen da ke tallafa wa Hamas ta fuskar tattalin arziki da siyasa.
Ƙasar da ta fi kowacce tallafa wa Hamas ta fuskar tattalin arziki da siyasa ita ce Qatar.
Dididah Belyoun, mataimakin shugaban cibiyar kula da harkokin duniya da tsare-tsare, a baya-bayan nan ya ce Hamas na samun tallafin dala miliyan 30 a kowane wata daga Qatar.
Ya ce ƙungiyar na amfani da kuɗin wajen biyan albashi ga ma'aikatan gwamnati a Zirin Gaza.
To sai dai a lokacin bazarar da ta wuce, an ruwaito cewa Hamas ba ta iya biyan albashin ma'aikata sabada rashin zuwan tallafin Qatar a kan kari.
A shekarar 2018 Jaridar 'Liberation' da ƙasar Faransa, ta ruwaito cewa a shekara 2014 hukumar tallafin kudi ta Qatar ta fara dakatar da tallafin jinƙai da take bai wa Gaza.
Dangane da wanan dalili Qatar ta riƙa bayar da tallafi ga Hamas ta hannun Isra'ila kuma wannan ba wani abun ɓoyewa ba ne.
Tallafin Qatar
Qatar ta kasance babbar mai tallafa wa Hamas. Shugaban Hamas Ismail Haniya na zaune a birnin Doha tun 2012.
Kuma ofishin shugabancin ƙungiyar na a babban birnin Qatar
Cibiyar nazarin ƙasashen Larabawa da ke Washinton ta ce Qatar ta samar da tallafin kusan dala biliyan 1.3 ga Gaza tsakanin 2012 zuwa 2022.
Cibiyar ta ce cikin shekara 20 da suka gabata, ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ta bayar da tallafin dala biliyan biyu ga Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma gwamnatin Mahmoud Abbas.
Ita kuwa Algeriya ta tallafa da dala miliyan 908, sai Kuwait mai dala miliyan 758, yayin da Saudiyya ta bayar da dala biliyan huɗu da miliyan 766.
Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ta alƙawarta bayar da wani ɓangare na kuɗin ga yankin Zirin Gaza, kuma kawo yanzu tana cika alƙawarinta.
Dangantaka tsakanin gwamnatin Masar da Hamas ya bambanta
Hamas ta fara a yankin Falasɗinawa a matsayin reshen ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta 'Ikhwanul Muslimeen'.
Ƙungiyar 'Ikhwanul Muslimeen' kungiyar addinin musulunci ce da aka ƙirkira a Masar cikin shekarar 1928.
Masar na da dangantaka mai ƙarfi da yankin Zirin Gaza, to sai dai dangantakar ƙasar da Falasɗinawan da ke zaune a Masar ya samu rauni tun lokacin da shugaba Abdul Fattah Alsisi ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2013.
Masar ta kasance wurin tsallakawa mafi muhimmanci ga Hamas. Akan shigar da abinci da kayayyaki masu tarin yawa zuwa Gaza daga Masar.
Majalisar lura da harkokin ƙasashen ƙetare da Amurka, ta ce a shekarar 2021, Hamas ta samu haraji na fiye da dala miliyan 12 daga kayyakin da ake shigarwa yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Kamar Masar, Turkiyya ta kasance mai tallafa wa siyasar Hamas, to sai dai babu ƙwaƙƙwar hujjar da ke nuna cewa Turkiyya na tallafa wa Hamas da kuɗi.
Turkiyya da Iran
Kafar yaɗa labaran Isra'ila ta Haaretz ta ce akwai yiwuwar Turkiyya na tallafa wa Hamas da dala miliyan 300 a kwacce shekara.
Baya ga haka, a cikin watan Yuli wasu jami'an Isra'ila suka an ƙwace tan 16 na abubuwan fashewa da aka aike daga Turkiyya zuwa Gaza.
To amma babbar ƙawar Hamas da ke tallafa mata ta fuskar soji da tattalin arziki ita ce Iran.
A baya-bayan nan babban mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro, Jack Sullivan, ya ce "mun faɗa tun da farko cewa Iran ce babbar mai tallafa wa Hamas da maƙudan kuɗi, domin ita ce bayar da mafi yawan kudin da ƙungiyar ke kashewa ta fuskar aikin soji.
Su ke bai wa sojoinsu horo da kayan aikin soji. A ɗaya ɓangaren kuma a baya-bayan nan shugaban hukumar tarayyar Turai ya ce kashi 93 na harsasan Hamas tana samunsu ne daga Iran.
Tallafi daga ƙungiyar agaji
Wani rahoto da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ta ce Iran na bai wa Hamas tallafin dala miliyan 100 a kowace shekara.
Babbar hanyar da Hamas ke samun kudi ita ce ta hanyar tallafin ɗaiɗaikun mutane a ƙasashen duniya, ƙungiyoyi da cibiyoyin tallafi.
A watan Fabrairun da ya gabata ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Hamas ta samu tallafin kuɗi daga ƙasashen yankin gulf da Falasɗinawa da ke zaune a wasu ƙasashe da kungiyoyin agajin Falasdinawa.
Cikin watan Janairun 2021, kamfain dillancin labaran Rasha na 'Sputnik' ya ruwaito cewa Hamas ta samu fiye da kashi 95 na kuɗaɗen da take kashewa daga gwamnatoci da masu kudin ƙungiyar Ikhwanul Muslimeen, da kuma magoya bayan Falasɗinawa a faɗin duniya.
Manyan ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke tallafa wa Hamas, sun haɗar da ƙungiyoyin agaji irin su 'Al Ansar'.
Al Ansar ƙungiya ce da ke da alaƙa da ƙungiyar ISIS, wadda aka kirƙira a shekarar 2001, kuma take bayar da tallafi ga yankunan Falasɗinawa, musamman a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
A shekarar 2016, gidan talbijin Al Alam TV ya gode wa Nasser Al Sheikh Ali, mataimakin gidauniyar Ansar, kan tallafin kuɗi da shugabannin Iran ke bai wa Iran.
A shekarar 2018, shafin Al Monitor ya ambato Sami Abu Ayaz na cewa, "Iran ta samar da tallafin kuɗi ga iyalan Falasɗinawa 9,000, inda kusan mutum 7,000 daga ciki ke zaune a Gaza, sai 2,000 ke zaune a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Cikin watan Yulin 2017, Al Ansar ta wallafa irin tallafin da Iran ke bai wa ƙungiyar a shafin Facebook.
Ya ƙara da cewa iyalan ma'autara da suka mutu sun samu tallafin kudin da ya yi daidai da dala 600, yayin da iayaln wasu da suka mutu ke samun aƙalla kudin ya ya yi daidai da dala 300.
Samun kuɗi ta hanyar zuba jari
Daya daga cikin manyan harkokin kasuwancin Hamas shi ne kasuwa kudin kirifto ta duniya.
Sakamakon yadda kungiyar ke gudanar da ayyukanta a asirce wurare irinsu harkokin kasuwancin Kirfito da kudin intanet, na iya taimaka wa ƙungiyoi irin su Hamas zuba jari a harkokin, kamar yadda mujallar 'Wall Street Journal' ta wallafa a baya-bayan nan.
Mujallar ta ce Hamas ta samu aƙalla dala miliyan 41 daga jarin da take zubawa a harkokin kirifto a shekara bakwai da suka wuce.
Mujallar ta ci gaba da cewa Hamas ta karɓi miliyoyin daloli na tallafin kuɗi daga kasuwar kirifto.
Daga nan ne sahen kirifto na Amurka ya ɗauki matakin ƙaƙaba dokoki masu tsari ga ayyukan Hamas a kasuwar.
Kuɗin tallafa wa ta'addanci
Atom Robinson, mai kamfanin Elliptic, da ke bincike kan ci gaban kasuwancin kudin intanet, kuma a baya-bayan nan ya ce Hamas ta zama daya daga cikin manyan masu amfani da harkar kirifto wajen ɗaukar nauyin 'ta'addanci'.
Haka kuma wani kamfani takwaransa mai suna 'TRM Libs', ya ce Hamas ta samu taimakon fiye da dala miliyan huɗu daga kamfanonin kirifto a shekarar 2021 kawai.
Hakan nan ita ma ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi iƙirarin cewa Iran ta bayar da tallafin kuɗi ga Hamas ta hanyar harkar kuɗin kirifto. To sai dai a 'yan watannin baya-bayan nan harkokin kirfton ƙungiyar na samun gagarumin koma baya.
A cikin watan Yuli hukumar yaƙi da ta'addanci ta Isra'ila ta ƙwace kuɗaɗen kirfto masu yawa da ke da alaƙa da ƙungiyoyin rajin tallafa wa Hamas.
Zuba jari a wasu ƙasashe
Hukumar yaƙi da ta'addanci ta Isra'ila ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin kuɗaden da suka ƙwace na wani kamfanin musanya da tura kuɗaɗe ne.
Hamas ba ta iya kashe duka kuɗaɗen da ta samu, a maimakon haka tana ware wani kaso mafi yawa domin zuba jari a ƙasashe duniya.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Hamas na taskance kuɗin da take samu daga Iran a ma'aikatar zuba jari, ta inda suke zuba jari a ƙasashen duniya masu yawa.
Ta ƙara da cewa an zuba jarin miliyoyin daloli a ƙasashen duniya irin su Sudan da Algeriya da turkyya da Haɗaɗɗiyar daular Larabawa da wasu ƙasashe.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta kuma ce manyan shugabannin kungiyar ne ke kungiyar.
Ta hanyar ribar da ƙungiyar ke samu daga jarin da ta zuba, shugabannin kungiyar ke samun damar gudanar da rayuwa ta alfarma.