BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Dalilin da yasa wasu 'yan Taiwan ke cikin mayakan Ukraine

42474090 Hoton alama

Tue, 13 Dec 2022 Source: BBC

A wata Majami’a a yammacin birnin Laviv da ke Ukraine, mahaifiyar Tseng Sheng-guang ce ke yi wa ɗanta kallon karshe da ke kwance a cikin akwatin gawa.

Tana tare da ‘yan uwa da wasu ‘yan kasar Ukraine da suka zo don yin bankwana da gawar mutumin, wanda ya mutu a nisan mil dubu nesa da gida, a yayin da ya ke yi wa kasar da bai taba ziyarta ba hidima.

“Sheng-guang ɗana, ina son in sanar da kai cewar kai jarumi ne,” daga bisani ta ce. “Za ka ci gaba da kasancewa dan da nake alfahari da shi.”

Mr. Tseng na yaki ne da dakarun kasa da kasa na Ukraine da ke tsare kan iyakar kasar, a lokacin da aka halaka shi a watan da ya gabata a garin Lyman da ke gabashin kasar.

Shi ne dan kasar Taiwan na farko da ya mutu a matsayin sojan kasar Ukraine.

A wata sanarwa da ma’iakatar kula da harkokin kasasehn kasar Taiwan ta fitar ta bayyana Mr Tseng wanda “ya saudakar da rayuwarsa don shiga yakin 'yancin da Ukraine ke yi.”

Dubban sojojin kasashen ne suka tafi kasar Ukraine don taya ta yaki, sai dai adadin 'yan Taiwan da suka zabi shiga cikin dakarun Ukraine ba su da yawa, don ba su wuce 10 ba.

Mamayar da Rasha ta yi ta janyo hankalin kasar da ke tsibiri, da sauran kasashen duniya.

China tana da’awar cewar Taiwan yanki ne na kasarta, kuma ta ci alwashin sai ta dinke ta, ko ta yi amfani da karfin idan har hakan ya zama tilas.

Taiwan na kalon kanta a matsayin 'yantacciyar kasa.

An dai sami karuwar ci gaba da samun ɗar-ɗar a yakin tun bayan ziyarar da ‘yar siyasar nan ta Amurka Nancy Pelosi a cikin watan Augusta, wanda hakan ya tunzura Beijing. China ta mayar da martani da kai hare-hare a tsibirin.

Sammy Lin, wanda aboki ne ga Mr Tseng d suka hadu a dandalin sadarwa, ya ce abokin nasa ya na nuna damuwarsa cewar akwai yiwuwar Taiwan ta fuskanci irin abin da Ukraine ke fuskanta.

“Na tuna, irin abun da yake fadawa abokansa, cewa shi bazai iya tsayawa ya na kallon yadda dakaarun Russina ke cin zarafi tare da kashe mutanen Ukraine.”

Mr Lin  y ace Mr Tseng “na cikin mutanen da ke kan tafarkin gaskiya” da ya taba haduwa da shi.

Taiwan na da tsarin bai wa 'yan kasar horo soji na tilas, wanda dukkan wadanda suke kammala karbar horon damar shiga cikin dakarun Ukraine yankin kasar waje.

Jack Yao, mai shekaru 28, na cikin wadan suka yanke shawarar tafiya. Ya iso Ukraine kwanaki 3 bayan da shugaban kasar Volodymyr Zelensky, ya roki yan sa kai na kasashen waje da su shiga yakin da Ukraine sin ke yi, farawa tun daga Taipei zuwa Poland sannan zuwa babban birnin kasar Kyiv.

"Ina kallon lamarin tun daga shekarar da ta gabata, tun bayan da Rasha ta dauki sojoji masu yawa da tankokin yaki, zuwa kan iyakarsu da Unkraine.

Babu wanda ya taba kawowa cewar hakan zai faru”, kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Yanayin da ake ciki a Taiwan, iri daya ne da wanda yake can. Tunanina ta wacce hanya zan iya taimakon Ukraine.”

Ya shiga dakarun Georgia na kasar waje, kuma an ba shi aiki na musayar wuta, lokacin da ya iso, Rasha na ta kokarin karbe iko a Kyiv.

"Ana ta kai hare-haren bama-bamai a sanda dakarun Rasha na Bucha”.

"An taba turani wani yaki, na ga an kashe daya dgaa cikin mutanenmu, a wani bam da ya tashi. Tsakaninmu da inda bom din ya tashi bai wuce mita 50 ba, a bayanmu”.

A lokacin da aka sami hutu yakan bayar da labarin Taiwa da abokan aikinsa.

Daya daga cikin wadan muke yaki da su, ya taba zama a Taiwan, tsawon shekara biyu, kuma yasan yanayin da ake ciki a can, Taiwan da Ukraine kamar 'yan uwa suke.

Suna fada mun cewar in gama wannan yakin in koma in kare kasarmu“.

Tuni Mr Yao ya koma Taiwan, yana ci gaba da sana'arsa ta sayar da gahawa, yayin da sauran ke can.

A cikin wani faifan bidiyo na baya-bayan nan na tallafawa Ukraine wasu 'yan Taiwan biyu sun bayyana ra’ayinsu.

“Babban abin da ya kawo mu Ukraine shi ne bai wa 'yan Ukraine kariya", yayin da suke rike da tutar Taiwan.

"Muna fargabar cewar idan Rasha ta yi nasara, China za ta yi haka a kan Taiwan. Don haka muna fatan mu zo Ukraine domin sadaukar da rayukanmu don yanci da tabbatar d alafiyar mutanen dake nan."

Duk da haka har yanzu akwai ‘yan taiwan masu yawa da suka je Ukraine, na da siyasar yankinsu a rana su.

A watan Yuni Li Xhenling ya sanadar da sashen China na BBC ya je can ne don ya sami "rayuwar da zai ringa tunawa da ita."

Shugaban kasar Amurka joe Biden ya nanata cewar Amurka za ta bai wa Taiwan kariya idan har China ta kai mata hari.

Sai dai tsarin shugabanin Washington shine ba su mayar da hankali kan bai wa Taiwan kariya ba, ba su kuma yanke wata shawara ta daban ba.

A watan da ya gabata Mr Biden ya ce bai yarda cewar China za ta shiga Taiwan abu ne mai yiwuwa ba.

Hakan ya biyo bayan wata ganawar gaba da gaba tsakanin shugaban China Xi Jinping gabanin babban taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a Bali.

'Yan Tiwan na bayyana ra'ayoyi daban-daban kan yiwuwar barkewar rikicin, a cewar Paul Huang na Inuwar ra'ayoyin Al'ummar Taiwan.

"Wani abun mamaki shi ne yadda karin mutanen Taiwan ko kadan ba sa nuna damuwarsu" kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Kamar yadda muka gani a Ukraine, mutane nawa ne suka nuna damuwarsu kan ko zai shafi rayuwarsu kai tsaye idan wani abu ya faru, kuma ko da kuwa ba su shirya masa ba".

Da dama daga cikin 'yan Taiwan ba su da tunanin cewar tsibirin zai iya ficewa daga China matukar Ukaraine ta ci gaba da kalubalantar Rasha.

A yayin da take ci gaba da alhini, mahaifiyar Mr Tseng ta ce matakin ɗan nata na yaki a cikin sojojin Ukraine ya ba ta wani nau'in kwanciyar rai.

"Sanin cewar a wani bangaren na rayuwarsa ta karshe, Sheng-guang ya tsaya ya yi yaki tare da jarumai marasa tsoro, da suka tallafi junansu kuma suna tare a raye ko a mace, duk kuwa da cewar ina jin ciwon mutuwar tasa, amma ana ta rarrashi na.

Source: BBC