BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Dan Yalon Tula ya buge Autan na Aisha a Maraba

18866102 Dan Yalon Tula ya buge Autan na Aisha a damben naira 100,000

Mon, 11 Dec 2023 Source: BBC

Dan Yalon Tula ya buge Autan na Aisha a damben naira 100,000 ranar Lahadi a Marabar Nyanya a jihar Nasarawa Najeriya.

Shi dai Autan na Aisha Guramada ya yi wata bakwai a tsaye a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke 'yan tifa a jihar Nasarawa.

Tun farko mawakin 'yan dambe Labaran dan gwamba ya kira Autan na Aisha ya yi masa kida, sannan masu goyon bayan dan wasan suka bashi kudi.

Shi kuwa Dan Yalon Tula daga Arewa da Labaran ya buga takensa a cikin fili ya tsaya bai je gabansa.

Daga nan suka shiga fili alkalin wasa Anas Dandume ya daga hannunsu sama da cewar sune a kan layi.

Turmin farko ba a yi wata bajinta ba bayan minti uku da suka yi, daga nan aka bukaci su huta kafin a koma turmi na biyu.

Bayan da suka shiga turmi na biyu ne wasa ya canja, inda Dan Yalo ya dunga bin Autan na Aisha, wanda ya dunga fita daga filin wasa.

Nan da nan Dan Yalon Tula ya rutsa dan damben Guramada a dab da inda nake zaune ya kuma buge shi, amma da kansa Autan na Aisha ya mike ba tare da kanikanci ba.

Nan da nan fili ya dauki sowa aka yi ta murna, bayan da a karon farko Autan na Aisha ya fadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka kisa:

  • Rabe Bahagon Ebola ya kashe Dan Aliyu
  • Bahagon Ali Kawoji ya doke Bahagon Aliyu
  • Dogon Mamman ya buge Dogon Basiru
  • Bahagon Ali Yalo ya yi nasara a kan Salama
  • Shagon Dan Aliyu ya doke Shagon Terminator
  • Ilele Garkuwan mai Caji ya buge Garkuwan Yahayan Tarasa


Sakamakon wasannin da aka yi canjaras:



  • Autan Kudawa da Ghali Shagon Shagon Mai Takwasara
  • Shagon Autan Dan Bunza da Alaye
  • Shagon Duna da Shagon Lawwalin Gusau
  • Bahagon Ali Kawoji da Autan Fafa


Source: BBC