BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

De Bruyne baya cikin 'yan City da za su buga Uefa Super Cup

Kevin De Bruyne

Mon, 14 Aug 2023 Source: BBC

Kevin De Bruyne baya cikin 'yan wasan Manchester City da za su buga mata Uefa Super Cup ranar Laraba.

Ranar Laraba Manchester City za ta kara da Sevilla a Uefa Super Cup, wanda zai zama labulen bude kakar bana ta gasar Turai.

Dan wasan tawagar Belgium ya ji rauni ranar Juma'a lokacin da City ta doke Burnley 3-0 a wasan farko a kakar Premier League ta bana.

Har yanzu City ba ta fayyace girman raunin da dan kwallon ya ji ba, amma dai baya cikin 'yan wasa 22 da kungiyar ta bayyana da za su buga mata karawar.

De Bruyne yana daga cikin kashin bayan City, tun bayan da ya koma Etihad daga Wolfsburg a Agustan 2015 kan fam miliyan 55.

Haka shima Bernardo Silva, ba zai buga karawar ba, wanda ya yi fafatawa da Burnley.

Haka shima Ruben Dias, wanda bai buga karawar ranar Asabar ba, babu shi a fafatawar ta ranar Laraba.

Kalvin Phillips da kuma Jack Grealish, wadanda suka buga wa City wasa ranar Juma'a a Turf Moor, za su yi wasan na Uefa Super Cup.

Manchester City ta dauki Champions League, bayan da ta ci Inter Milan, ita kuwa Sevilla ta yi nasara a kan Roma.

Saboda haka za a buga karawar tsakanin wadda take da Champions League da wadda ta dauki Europa League a bara.

'Yan wasa 22 da za su buga wa City karawar

Kyle Walker, Kalvin Phillips, John Stones, Nathan Ake,

Mateo Kovacic, Erling Haaland, Jack Grealish, Aymeric Laporte, Rodrigo, Stefan

Ortega Moreno, Julian Alvarez, Sergio Gomez, Josko Gvardiol, Manuel Akanji,

Ederson, Maximo Perrone, Scott Carson, Phil Foden, Oscar Bobb, Cole Palmer, Rico

Source: BBC