Menu

De Gea ya lashe kyautar safar hannu ta gola ta zinare a Premier

David de Gea

Sun, 21 May 2023 Source: BBC

Mai tsaron ragar Manchester United, David de Gea ya lashe kyautar safar hannu ta gola a Premier League a bana, duk da saura wasa biyu ya rage a gabansa.

Dan kasar Sifaniya ya yi karawa 16 kwallo bai shiga ragarsa ba, yayin da guda 41 suka shiga raga a wasan da aka doke United a kakar nan.

Golan Liverpool, Allison shine na biyu, wanda kwallo bai shiga ragarsa ba a fafatawa 14, wanda ya ci karo da koma baya, bayan da Liverpool ta tashi 1-1 da Aston Villa ranar Asabar.

A dai ranar Asabar, United mai kwantan wasa ta doke Bournemouth 1-0 a karawar mako na 37 a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

Golan Newcastle, Nick Pope da na Arsenal, Aaron Ramsdale kowanne ya yi fafatawa 13 kwallo bai shiga ragarsa ba, yayin da na Manchester City, Ederson ya yi wasa 11 ba tare da an zura kwallo a ragarsa ba.

Wannan shine karo na biyu da De Gea ya karbi kyautar, bayan wadda ya lashe a 2017-2018.

Duk da wannan kwazon, De Gea na shan suka a kakar nan, wanda ake zargi da yawan yin kuskure da cewar lokaci ya yi a canja shi, bayan kaka 12 a United.

Kuskuren da golan ya yi ne Said Benrahma na West Ham ya ci United a wasan da aka doke ta 1-0, wanda karo na hudu kenan da ya yi haka a bana a Premier.

Sai dai Erik ten Hag ya ce kowa yana kuskure, ya kuma san cewar De Gea na kan ganiya, wanda ya tsare ragar United karo 542.

Kwantiragin United da De Gea zai kare a karshen kakar nan a Old Trafford.

Duk da wannan kyautar da De Gea ya lashe a kakar nan an ci golan kwallaye da yawa a karawa da Manchester City da Brentford.

Manchester City ce ta lashe kyautar kungiyar da ba a zura mata kwallaye da yawa a raga ba a kakar mai mai 31, sai Newcastle da aka ci kwallaye 32.

Source: BBC