Menu

Denmark na shirin haramta ƙona Ƙur'ani da sauran littafan addini

Hoton alama

Mon, 31 Jul 2023 Source: BBC

Ƙasar Denmark na shirin haramta gangamin kona Kur'ani da sauran litattafan addini masu tsarki saboda dalilan tsaro da kuma huldar diflomasiyya.

Ma'aikatar harkokin wajen Denmark ta ce duk da cewa kare 'yancin fadar ra'ayi yana da muhimmanci, zanga-zanga mai alaka da tsattsauran ra'ayi tana kawo barazana ga tsaro.

Ƙasar tana duba yiyuwar daukar matakan shari'a kan wasu abubuwan da ba ta amince da su ba, ciki har da batun zanga-zanga a gaban ofisoshin jakadancinta.

Firaministan Sweden ma ya ce sun fara aiki a kan wani abu mai kama da wannan.

Kasashen biyu sun fuskanci matsin-lamba a makonnin nan, bayan da hukumomi suka bayar da izinin gudanar da gangami, inda wasu suka kona Al-Ƙur'ani mai girma, lamarin da ya janyo matsalar difilomasiyya tsakaninsu da kasashen Musulmai.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Denmark ta fitar ta ce tana son kawo karshen yanayin da zanga-zanga za ta kai ga cin mutumcin kasa ko al'ada ko kuma addinin wasu, musamman wadda za ta iya haifar da illa ga Denmark.

Sai dai kuma, gwamnatin Denmark din ta jaddada matsayarta a kan mutumta 'yancin fadin ra'ayin jama'a kamar yadda dokar kasar ta yi tanadi.

Sanarwar ta kuma amsa cewa zanga-zangar cin mutumcin addini ta shafi mutuncin Denmark a duniya, ta kuma jaddada matsayar gwamnati ta yin Allah-wadai da kona litattafan addini.

Zanga-zangar dai ta kai wani matsayi da ake kallon Denmark ''kamar wata kasa mai goyon bayan cin mutumcin kasa ko al'ada ko kuma addinin wasu'' inji sanarwar.

A wata sanarwa ta daban, firaministan Sweden, Ulf Kristersson, ya ce kasarsa ta riga ta bi sahu don daukar irin wannan mataki, kuma tuni ya fara tattaunawa da takwaransa na Demark, Mette Frederiksen.

Ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa: "Mu ma mun fara nazari kan matakan shari'a...don fadada tsaron kasarmu, da tsaron jama'ar Sweden a ko'ina suke a duniya."

Sanarwar biyu na zuwa ne bayan cin mutumci da kuma kona Ƙur'ani mai girma da aka yi a makonnin nan.

A cikin watan Yuni, wani Kirista dan asalin Iraƙi da ke z a aune a Sweden ya kona Ƙur'ani a wajen babban masallacin Stockholm.

A makon da ya gabata ma, mutumin ya kara samun izinin kona littafin mai tsarki a karo na biyu, lamarin da ya tursasa rufe ofishin jakadancin Sweden a birnin Baghdad bayan masu zanga-zanga sun cinna masa wuta.

Bayan samun izinin na biyu ne kuma wasu 'yan Denmark biyu suka tattaka Ƙur'anin, suka kuma kona shi a kusa da tutar Iraƙi a gaban ofishin jakadancin ƙasar da ke birnin Copenhagen.

Source: BBC