Kungiyar kwararrun likitoci masu tiyatar zuciya a Najeriya, ta ce dubban mutane ne ke mutuwa a ko wace shekara sakamakon ciwon zuciya a kasar.
Kungiyar ta ce mace-macen na faruwa ne saboda rashin isassun asibitoci da kayan aiki da kuma ma'aikata da suka kware kan warkar da cututtukan zuciya.
Ma'ajin kungiyar na kasa Dakta Salisu Ismail ya shaidawa BBC cewa al'amarin yana da matukar tayar da hankali, kasancewar a duk shekara ana samun fiye da mutum dubu tamanin da suke bukatar a yi musu aiki a zuciya.
Ya ce "akwai yara da manya musamman masu larurar hawan jini wadanda suka manyanta da ke bukatar a yi masu tiyata, amma ba su da mafita a halin da ake ciki".
Likitan na zuciya ya ce a duk fadin Najeriya wurare da ake tiyatar zuciya 'ba su kai goma ba' duk da irin yawan marasa lafiya masu bukatar tiyatar.
Ya kara da cewa alamomin ciwon zuciya sun hada da wahalar numfashi da rashin kuzari wajen yin aikin karfi.
Sauran alamomin sun hada da yawan bugun zuciya bagatatan da
dagowar kirji ta bangaren hannun hagu da sauransu.
Da yake karin bayani kan abubuwan da ke haddasa ciwon zuciyar dakta Salisu ya ce akwai yara da ake haifarsu da matsalar baya ga su kuma akwai wasu kwayoyin cutuka da ke shafar zuciya.
Likitan ya ce idan mutum ya girma sosai wani lokaci hanyoyin jini su na toshewa tare da haifar da rashin numfashi yadda ya kamata.
Zuciya dai sassan jiki ce mai matukar muhimmanci ga dan Adam domin kuwa ita ke buga jini ga dukkan jiki domin mutum ya rayu.