0
MenuAfrica
BBC

Duke na Edinburgh: Kaunar da Yarima ke yi wa wasanni

Tue, 13 Apr 2021 Source: bbc.com

Watakila irin kazar-kazar din da Yarima Philip yake da shi a lokacin yarinta ne ya ba shi damar kutsawa cikin harkokin wasanni.

Saboda gwanintar da yake da ita da kuma yadda yake matukar son wasanni, hakan ya ba shi damar karawa a manyan matakai gami da taka rawa sosai a bangaren tsare-tsaren wasannin daban-daban.

Bayan matarsa ta zama sarauniya, sai ya kasance matukar son da yake yi wa wasanni ne ya sa har yake mantawa da wasu abubuwa da dama suke damunsa musamman a bangaren mulki.

Philip ya halarci makarantar Cheam, wadda ita ce makarantar kwana ta farko da ya yi a 1928.

Shugaban makarantar mai suna Harold Taylor mutum ne mai son wasannin motsa jiki, kwararre ne sosai, ga shi kuma gwanin doki, yakan karfafi guiwar dalibansa wajen yin wasanni daban-daban.

Philip ya yi fice sosai a tsakanin tsararrakinsa. Ya ci gasa da yawa a wasannin motsa jiki da ninkaya, haka nan kwararren mai tsaron raga ne a kulob dinsu na bal na makarantar.

Har ila-yau, yakan yi wasa Kiriket a wannan makaranta tun yana dan shekara 11.

A lokacin da ya kai shekara 13 ne aka mayar da shi makarntar Salem da ke kudancin Jamus, wadda sirikinsa Yaria Mad na Baden ya bude. Wani kwararren malami mai suna Kurt Hahn ne shugaban makarantar a wancan lokaci.

Akan fara hidimar karatu a kullum a makarantar ta hanyar wanka da ruwan sanyi, sannan a tafi gudu na rabin mil. Akan kara da 'yan tsalle-tsalle da sauran wasanni.

Malam Hahn ya yi amanna da cewa wannan motsa jikin na zahiri yana da matukar muhimmanci wajen sa yara su murmure daga sangartar samartaka.

Haka nan Malam Hahn ya ci gaba da horar da yaran nan har bayan da aka mayar da makarantar zuwa lardin Gordonstoun da ke arewacin Scotland.

Gallazawar da 'yan wariyar launin fata suka yi ne ya sa ya bar kasar.

Abokin Ninkaya

Malam Hahn ya yi amfani da damar da yake da ita, ta kasancewar makarantar tana kusa da (tafkin) Moray Firth, wanda hakan ya ba shi damar sa kowane yaro sai ya koyi ninkaya, haka kuma dole su dinga yin sauran wasannin da ake yi a filayen wasannin.

Taron jama'ar da ke halartar wannan wasan daga wurare daban-daban, ya kara wa Philip nacin son shawagi a kan ruwa, kuma hakan ya taimake shi sosai, domin sam ba ya fama da wasu cututtukan da suka shafi ruwa.

A lokacin da Philip ya auri gimbiya Elizabeth, a 1947, sai aka ba wa ango da amarya kyautar wani jirgin ruwa mai suna Bluebottle a matsayin kyautar murnar aure, amma fa ita sarauniya ba kasafai take bin mijin nata wajen yawo a jirgin ruwan ba.

Babban abokin Yarima a wajen yin fito shi ne Uffa Fod, wanda ya zama abokinsa sosai har lokacin rasuwarsa a 1972. Sukan yi tsere sosai tare da Fod a jiragensu na ruwa.

Akwai lokacin da Fod yake fada dangane da abokin fiton nasa: "Ban taba sanin wani da ya lakanci haye igiyar ruwa a jirgi, cikin kwarewa ba, sama da shi."

Haka dai Philip ya dinga kece raini a wassanin ruwa da ake yi da suka kebanci fada, kuma zuwansa yana kara wa wasannin armashi.

Kwarewarsa a wajen wasan Kiriket kuwa ya sa manyan mutane da dama sun dinga yaba masa a lokuta daban-daban.

Tsegumi

Kwararren dan wasan Kiriket din nan na kasar Australiya mai suna Sa Donald Bradman ya taba cewa, Philip kwararren badame ne a harkar wasan Kiriket, wanda ya kware sosai a tafiyar da wasan.

"Duk da cewa a yanzu ana cewa mu mutanen Austireliya ba mu da adalci, to don haka zan iya mika wadannan bayanan ga mutanen Birtaniya domin su duba su ga abin da muka bayyana na kwarewarsa."

Amma kuma a fannin kwallon doki, a nan ma fa, mai alfarma Yarima ya yi fice, ta yadda sai da ya zama daya daga cikin 'yan wasa hudu mafiya daukaka a Birtaniya a tsakiyar 1960, duk da cewa bai fara harkar wasan da wuri ba.

Ba wai kawai wasan ya iya ba, har sai da ta kai ya kara daga kimar was an, har ya kara shahara sosai. Duk lokacin da ya zo filin wasan, take za ka ji ana ta yamadidi da labarain wasan a wurare daban-daban.

Kamar yadda yake a dukkanin sauran wasanni, yakan zage sosai a wasan kwallon doki, kuma shi ma, wani lokacin akan samu akasi ya fado ko ya zame, kamar dai yadda abin yake a wasan kwallon doki.

An tilasta shi ya daina yin wasan kwallon doki a lokacin da ya sami hadarin kumburi a hannunsa, lokacin kuwa ya kai shekara 50. Amma duk da haka, sai ga shi ya sake komawa wani wasan saboda karsashin da yake da shi, wato wasan keken doki.

Tseren keken-doki fitaccen wasa ne a kasashe irin su Jamus da Hungary, amma wasan bai shahara ba a Birtaniya, don haka Philip ya yi yunkurin kafawa da tallata shi.

Tangarda a wasan Keken doki

Mai martaba ya kasance wani fitacce kuma jagora a wajen wasan tuka keken doki, ta yadda ya yi kokari sosai wajen kafa dokoki da daga likkafar wasan a kasar Birtaniya, sannan kuma ya dinga shiga gasa a rukunin wasan kasar.

Daga cikin abubuwan mamakin da suka faru a rayuwarsa ta wasanni shi ne yadda ya yi abota da George Bowman, wanda suke a rukuni daya.

Bowman ya taba cewa: "ni fa ba kowa ba ne, kuma shi ne fa Yarima, don haka wani lokaci za ka ga mutane suna cecekuce a kan abotar.

Amma bai taba nuna min wani bambanci dangane da hakan ba. Yakan dauke ni ba tare da wani bambanci ba.

"Wannan na daya daga cikin abubuwan da nake matukar so dangane da shi."

Duk da cewa an dan sami tataburza a lokacin da yake gudanar da wadannan wasannin, misali shi ne kamar wani lokacin da keken dokinsa ya bugi wani kankaren dutse, har sai da ya hantsila da su, amma wannan bai sa ya daina ba, har lokacin tsufansa.

A duk fadin rayuwarsa, ya yi ta fadi tashi wajen ganin ya karfafa guiwar wasu domin su ma su dandani lagwadar motsa jiki, yadda shi ma yake jin dadin hakan.

Yana matukar son kungiyar wasanni ta kasa, wadda ake kira da Fields in Trust, wadda ta dinga rajin karen hakkin samar da wadatattun filaye domin wasanni da harkokin motsa jiki.

Kyautarsa ta girmawa da ya samar wadda aka fara a 1956 a sakamakon horon da ya samu daga Kurt Hahn, ta kara azamar samari wajen kara dagewa da shiga ayyukan da suka shafi motsa jiki.

Saboda tsananin yadda yake son gasa, hakan ya bai wa Yarima Philip damar cimma babbar nasara a kusan dukkanin wani fannin wasannin da ya yi.

Duk da haka, za a iya ganin irin namijin kokarin da ya yi a fannin wasanni ta fuskar yadda ya kimsa wa matasa son harkar, da kuma irin goyon bayan da ya bayar ga kungiyoyin wasanni da yawa.

Source: bbc.com