BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

El-Ghazi ya shigar da ƙara kan sallamarsa daga Mainz

24628321 Anwar El-Ghazi

Wed, 15 Nov 2023 Source: BBC

Ɗan wasan ƙasar Holland Anwar El Ghazi na shirin ɗaukar matakin shari'a a kan tsohon kulob ɗinsa Mainz saboda korar da aka yi masa ba bisa ka'ida ba.

Mainz ta soke kwantiragin El Ghazi a ranar 2 ga Nuwamba bayan wasu jerin rubuce-rubucen da ya yi a shafukan sada zumunta game da rikicin Isra'ila da Gaza.

Mainz ta ce tawagar lauyoyin El Ghazi ne suka sanar da ita game da lamarin.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ƙara da cewa ba za ta ƙara yin tsokaci ba "domin shari'a ce da ke gudana a halin yanzu".

A halin da ake ciki kuma, BBC ta ga jerin sakonnin ɓatanci da aka aike wa ɗan wasan mai shekaru 28 a shafukan sada zumunta, da dama daga cikinsu sun haɗa da barazanar kisa ga ɗan wasan da iyalansa, da kuma kiransa da lakabin "ɗan ta'adda".

Wasu daga cikin sakonnin na cin zarafi sun fito ne daga mutane mazauna Birtaniya kuma an tura su zuwa sashin 'yan sanda na ƙwallon ƙafa na Birtaniya don gudanar da bincike.

Bayan kawo karshen kwantiraginsa, El Ghazi ya ce: “Na tsaya kan abin da ya dace, ko da kuwa yana nufin zan tsaya ni kaɗai.

Source: BBC