Empoli ta kori kociyanta, Paolo Zanetti za ta dawo da Aurelio Andreazzoli domin ya ci gaba da jan ragamar kungiyar.
Ranar Lahadi wasan makon na hudu a Serie A Roma ta caskara Empoli 7-0 da hakan ya kai kungiyar ta karshe a teburin babbar gasar tamaula ta Italiya.
Zanetti, mai shekara 40 tsohon dan kwallon Empoli an nada shi aikin a bara da ya kai kungiyar mataki na 14.
To sai dai kungiyar ta kasa cin kwallo, wadda aka zura wa 20 daga wasa hudun da aka fara a kakar nan ta Serie A.
Kafin ya karbi aikin horar da Empoli ya kai Venezia matakin Serie A daga karamar gasar kasar, amma aka sallame shi a Afirilun 2022.
An kore shi ne bayan an doke kungiyar wasa takwas a jere da ta yi kasan teburi daga baya ta fadi daga Serie A ta kakar.
Zanetti ya karbi aikin kocin Empoli daga Andreazzoli, wanda zai sake jan ragamar kungiyar karo na hudu.
Ya horar da kungiyar da samun tikitin buga Serie A a kakar 2018 daga baya ta fadi daga gasar kaka daya tsakani.
Ya sake kama ragamar horar da kungiyar a kakar 2021/22, wanda ya tserar da ita daga faduwa a gasar.
Mai shekara 69 ya horar da Ternana a Serie B, wadda ya karbi aikin a Disambar 2022, amma ya yi ritaya bayan hada maki 12 daga wasa 12.
Empoli ta bashi aiki a Yunin bara daga baya ya soke kwantiragin tun kan fara kakar nan.
Ranar Lahadi Empoli za ta karbi bakuncin Inter Milan, wadda take jan ragamar teburin Serie A a fafatawar mako na biyar.