BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

FBI ta kama sojan da ake zargi da fitar da bayanan sirrin Amurka na yaƙi

Matashin yana aiki ne da rundunar sojin saman Amurka

Fri, 14 Apr 2023 Source: BBC

Jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, sun kama wani matashi da ke aiki a sashen leken asiri na sojin sama na kasar bisa zargin fitar da takardun bayanan sirri na soji a kan yakin Ukraine.

An dai ga wasu hotunan bidiyo da aka dauka daga wani jirgin sama mai saukar ungula na ‘yan jarida na nuna jami’an hukumar binciken manyan laifukan Amurkar, FBI, wadanda suke cikin damara da makamai a wani wuri mai bishiyoyi, a lokacin da suka kama shi.

Jim kadan da kama shi ne sai Babban Lauyan gwamnatin Amurka, Atoni Janar Merrick Garland ya yi sanarwa kan kamun;

Ya ce, ‘’A yau Ma’aikatar Shari’a ta kama Jack Douglas Teixeira a bisa alaka da binciken da ake yi na zargin dauka rikewa da kuma yada bayanan tsaro na sirri na kasa ba bisa ka’ida ba Teixeira ya shiga hannun jami’an FBI, ba tare da wata matsala ba.''

Za a gurfanar da shi da farko a kotun gunduma ta Amurka ta Massachusetts, jihar da sansanin da yake aiki yake.

Tuni kafafen yada labaran Amurka suka fara bayyana matashin a matsayin babban wanda ake zargi da satar fitarwa da kuma yada wadannan bayanai na sirri.

Ana zargin shi ne jagoran ‘yan wani dan gungun masu mu’amulla a wani shafin sada zumunta da muhawara na intanet, wadanda ke sha’awar bindigogi da kayan soji da kuma kaunar Ubangiji kamar yadda wani daga cikin mambobinsu ya bayyana.

An ce mutumin ya samu wadannan bayanai na sirri ne a sansanin sojin da yake aiki, inda daga nan ya fara yada su a tsakanin abokanansa na wannan shafi, amma kuma daga karshe bayanan suka fita ga sauran jama’a.

Bayanai sun nuna abokanansa a shafin sun kunshi daidaikun mutane a Rasha da kuma Ukraine.

Sannan ya fara yada bayananan ne tun farko-farkon lokacin kullen annobar korona, a 2020.

Jaridar Washington Post, wadda ta yi magana da wani daga cikin abokan mutumin, wanda ba ta bayyana sunansa ba ta ce ya shaida mata cewa ba wai mai kwarmata bayanai ba ne kuma ba shi da wata alaka da gwamnatin wata kasar waje.

Ana ganin kama shi da aka yi zai sa a tsananta bincike kan wanda wadannan bayanai na sirri suka je hannunsa.

Bayanan na sirri dai sun nuna yadda Amurka ke nazari a kan yakin Ukraine da kuma wasu abubuwa na sirri na kawayenta.

Lamarin da ya kasance tonan silili da ya kunyata gwamnatin Amurkar tare da jefa harkar tsaron kasar cikin hadari.

Source: BBC