BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Fafaroma Francis ya buƙaci ƙasashen Turai su daina tatsar ƙasashen Afirka

Fafaroma Francis da shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo Felix Tshisekedi

Wed, 1 Feb 2023 Source: BBC

Jim ƙadan bayan saukar sa a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Fafaroma Francis ya gabatar da jawabi mai cike da Alla-wadai na yanda ake cin dunduniyar ƙasar da ma nahiyar Afirka na tsawon ƙarni.

Ya kuma yi magana kan mamayar siyasa da ke janyo ɗebe tattalin arzikin ƙasashen da mayar da mutane bayi.

A wani bangare na jawabinsa, ya faɗa wa ƙasashen duniya da su san da irin bala’o’i da aka haddasa a ƙasar da kuma girmama mutanen wurin.

"A kyale Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, a ku kuma kyale Afirka da daina gallaza mata, ba ma’adinai ba ne da za a ce za a ɗebe ko kuma wuri da za a yi wa ganima,’’ in ji Fafaroma Francis, yana mai nuni da ɗimbin albarkatun ƙasa da suka jawo rikici da kuma mutuwa a ƙasar.

Sai dai, Fafaroma bai yi tsokaci kan irin rawar da masu mulkin mallaka na Katolika suka taka ba, tare da goyon bayan hukunce-hukuncen tarihi na fadar Vatican da kuma ta’asar da suka aikata a nan.

Nuna damuwa kan ziyarar Fafaroma

Ya yi magana kan son kai da wasu manya ke nunawa a baya-bayan nan a Jamhuriyar Dimokurɗiyyar Kongo, "an ɗebe arzikin ƙasar," yana mai nuni da kusan mutane miliyan bakwai da aka yi kiyasin an kashe a rikicin ƙasar cikin shekaru 30 da suka wuce.

A lokacin da aka fara wannan tafiya a shekarar da ta gabata, Fafaroman ya yi shirin kai ziyara a gabashin wannan ƙasa inda mafi munin tashe-tashen hankula suka ɓarke da kuma wajen da miliyoyin mutane suka rasa matsugunansu.

Amma ya ɗage tafiyar zuwa yanzu saboda rashin lafiya da ya yi fama da ita, kuma yanzu matsalolin tsaro na nufin ba za a iya tafiya zuwa gabas ba.

A cikin jirgin da ya taso daga birnin Rome, Fafaroma Francis ya sanar da ‘yan jarida cewa ya yi nadama cewa bai samu damar bi ta kan hanya domin gaishe su baki ɗaya ba kamar yadda ya saba yi, inda ya roki mu ci gaba da tafiya.

Karon farko da jama'a suka ga Fafaroma a lokacin da ya sauka a Kinshasa shi ne a cikin keken guragu, amma duk da alkawarin rage jadawalin balaguron ƙasa da ƙasa da ya fito karara a 'yan watannin nan cewa wannan tafiya shine fifiko ga Fafaroma Francis.

Daga baya a cikin makon nan, Fafaroman zai kai ziyara Sudan ta kudu tare da Babban Limamin cocin Canterbury, da kuma jagorantan cocin Scotland.

Ana tunanin cewa zai yi kira ga shugabannin siyasa bayan wani taro a fadar Vatican da su ƙara kaimi wajen samar da zaman lafiya a wata kasar mai fama da rikici.

Source: BBC