Menu

Faransa ta zura ƙwallo mafi yawa a tarihinta na tamaula

57839708 Kylian Mbappe ya zira kwallo uku a gasar

Sun, 19 Nov 2023 Source: BBC

Tawagar Faransa ta sharara ƙwallo 14-0 a ragar Gibraltar a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai, Euro 2024 ranar Asabar.

Tawagar ta ci ƙwallo bakwai a zagayen farko, sannan ta ƙara wasu bakwai a zagaye na biyu, hakan ya sa ta ci kwallo mafi yawa a tarihinta.

Tun kan karawar Faransa ta samu gurbin shiga gasar da za a yi a Jamus a baɗi, amma hakan bai sa ta ɗauki wasan da sauki ba, inda Kylian Mbappe ya ci uku rigis.

Matashin ɗan wasa, Warren Zaire-Emery yana daga cikin 'yan wasa bakwai da kowa ya zura kwallo a raga a minti na 45 din farko.

Mai shekara 17 da wata takwas da kwana 11 ranar Asabar ya zama matashin ɗan ƙwallon Faransa da ya taka mata leda tun bayan 1914.

Shi ne ya zura ƙwallo na uku a karawar, wanda ya ji rauni aka kuma canja shi.

Ethan Santos ne ya fara cin gida, wanda daga baya aka bai wa jan kati a fafatawar, Marcus Thuram ya ƙara na biyu.

Kylian Mbappe ne ya zura na huɗu a raga a bugun fenariti, bayan da Zaire ya ci na uku, sauran da suka ci kwallayen, Clauss da Kingsley Coman da kuma Youssouf Fofana.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne kamar Faransa ta hakura da cin ƙwallaye, sai Adrien Rabiot ya ci na takwas.

Daga nan aka ci gaba da ɗura wa Gibralta ƙwallaye ta hannun Coman da Ousmane Dembele sannan Mbappe ya ƙara biyu.

Kafin a tashi wasan shi ma Olivier Giroud ya ƙara biyu daf da za a tashi wasan.

Faransa ta ƙarasa wasan da kai hare-hare 39, yayin da Gibralter ba ta kai ko ɗaya ba.

Source: BBC