Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa ta sanar cewar ƙungiyoyi 32 ne za su riƙa buga gasar Fifa Club World Cup daga 2025.
Amurka aka bai wa izinin karɓar baƙuncin wasanninda za a fara daga 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli.
Kenan Amurka - wadda za ta shirya gasar Copa America a baɗi - za ta ci gaba da shirin haɗakar karɓar baƙuncin gasar Kofin Duniya da Mexico da Canada a 2026.
Sabon fasalin wasannin zai ƙunshi ƙungiyoyi daga nahiyoyi shida, yayin da 12 daga nahiyar Turai za riƙa wakiltarta a gasar.
Chelsea da Real Madrid da Manchester City sun samu tikitin shiga wasannin kai tsaye,domin suna daga cikin waɗanda suka ɗauki Champions League a shekara huɗun nan.
Ita ma Arsenal za ta samu shiga gasar da zarar ta lashe gasar zakarun Turai ta bana.
Bayern Munich da Paris St-Germain da Inter Milan da Porto da Benfica duk za su buga gasar ta baɗi, saboda maki mai yawa da suka haɗa a wasannin ƙungiyoyin Turai.
Shugaban hukumar Fifa, Gianni Infantino ne ya sanar da wannan sabon fasalin Fifa Club World a wani taro a Jeddah, Saudi Arabia ranar Lahadi.
Ana buga Fifa Club World Cup a duk shekara, inda ƙungiyoyi bakwai daga nahiya shida ke buga wasannin.
Manchester City, mai riƙe da Champions League na bara za ta kara da Urawa Red Diamonds a wasan daf da ƙarshe ranar 19 ga watan Disamba a Saudi Arabia.