Kwamintin Fifa, wanda ya dakatar da Luis Rubiales shekara uku na duba yadda zai kara tsaurara matakan hukunta shi.
An dakatar da Rubiales, mai shekara 46 cikin watan Oktoba, bayan da ya sumbaci Jenni Hermoso a lebe a lokacin da Sifaniya ke murnar lashe kofin duniya.
Daga baya Rubiales ya yi murabus a cikin watan Satumba, bayan da ya ki amincewa ya sauka daga mukamin shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya.
Shi dai Rubiales ya ci gaba da cewar da amincewar 'yar wasan ya sumbace ta a fili, kuma duk wanda ya kalli hakan ta wata siga mutumin banza ne.
An yi ta cece-kuce kan batun sunbatar 'yar wasan da Rubiales ya yi ya karade duniya, inda batun ya hana a kalli kwazon da Sifaniya ta yi wajen lashe kofin.
Sifaniya ta doke Ingila 1-0 ta dauki kofin duniya a gasar da aka yi a Australia da New Zealand a shekarar nan.