BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Firaministan Isra'ila ya yi watsi da kiran shugaban Amurka

Firaminista Netanyahu ya ce babu wani daga waje da zai matsa musu

Wed, 29 Mar 2023 Source: BBC

Shugaba Joe Biden na Amurka ya bukaci Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya yi watsi da shirin gwamnatinsa na sake fasalin bangaren shari'a, kudurin da ya janyo ake ta zanga-zanga a fadin kasar ta Isra'ila.

Sai dai a martaninsa Mista Netanyahu ya ce ba zai mika wuya ga wani matsin lamba daga waje ba.

A lokacin da Firaministan Isra’ilar a farkon makon nan ya furta cewa za a jinkirta shirin yi wa bangaren shariar sauye-sauye, fadar gwamnatin Amurka ta ce kamata ya yi firaministan na Isra’ila ya nemi sasanto a kan maganar.

To amma a wannan karon Shugaban na Amurka Joe Biden ya dara waccan maganar da cewa yana fata Mista Netanyahu ya yi watsi da wannan shiri, na neman raba alkalan Isra’ila da iko.

Mista Biden na magana ne ga manem alabarai a karshen ziyarar da ya kai North Carolina:

Ya ce, ‘’ kamar da dama magoya baya masu karfi ni ma na damu sosai, na damu da fatan ganin cewa sun fahimci lamarin nan kai tsaye.

Ba zai yuwu su ci gaba da bin wannan turba ba, kuma na nuna hakan karara.

Da fatan Firaministan zai yi yadda zai yi kokarin samun sasanto da ya dace, amma dai mun zuba ido mu ga hakan.’’

A martaninsa Mista Netanyahu ya ce a matsayin Isra'ila na kasa mai cin gashin kanta tana yanke wa kanta shawar da ta dace da ita, daga abin da al'ummarta suke so amma ba daga wani matsin lamba daga waje ba, ciki har da babbar kawarta.

Yayin da ake wannan shugaban kasar Isra’ilar, Isaac Herzog, ya kira taron wakilan gwamnatin hadakar da kuma na jam’iyyun hamayya domin tattaunawa ta farko a kan shirin gwamnatin na yi bangaren shari’ar garambawul.

Shugaban ya yi hakan ne yayin da Firaminista Netanyahu ya ce za a dakatar da gabatar da kudurin ga majalisar dokoki domin amincewa da shi don a samu a tattauna a kai.

Jagororin ‘yan hamayya Yair Lapid da Benny Gantz, sun ce bangarorinsu tuni sun shirya domin tattaunawar.

Ana ci gaba da zanga-zanga a fadin Isra’ilar da aka shafe makonni ana yi a kan shirin, wanda masu zanga-zangar ke son ganin gwamnati ta yi watsi da shi gaba daya.

Source: BBC