BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Firaministar Birtaniya ta sauka daga muƙaminta

91166294 Liz Truss

Thu, 20 Oct 2022 Source: BBC

Firaministar Birtaniya Liz Truss ta sauka daga muƙaminta bayan kwana 45 da hawa kan mulki. Ƴan majalisa na jam'iyyar Conservatives sun buƙace ta da ta ajiye mulki bayan da gwamnatin tata ta ci karo da matsaloli. Ajiye muƙamin nata ya zo ne bayan da wata minista mai matuƙar muhimmanci ta ajiye aiki, yayin da ƴan majalisa na jam’iyyar Conservatives suka yi mata bore. A watan Satumba ne aka zaɓi Truss a matsayin firaminista, sai dai kwarjininta ya yi ƙasa bayan soke wasu daga cikin tsare-tsaren da ta ɓullo da su.

Source: BBC