Menu

Fitattun 'yan wasa biyar da ba su taba lashe gwarzon Afirka ba

34704774 Victor Osimhen, Achraf Hakimi da Mohamed Salah

Mon, 11 Dec 2023 Source: BBC

Ana sa ran dan wasan Najeriya, Victor Osimhen na kan gaba da za a bayyana gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2023 a ranar Litinin.

Sai dai dan wasan Napoli na fuskantar kalubale daga dan wasan Liverpool, Mohamed Salah da na Paris St-Germain, Achraf Hakimi.

Dan kasar Masar ya lashe kyautar a 2017 da kuma 2018 da yin na biyu biye da Sadio Mane a 2019 da kuma 2022.

Shi kuwa mai tsaron bayan tawagar Morocco, Hakimi ya taka rawar gani a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, bayan da kasar ta kai daf da karshe a wasannin.

Osimhen wanda ya yi sawun gaba a matakin takarar Ballon d'Or a kyautar da aka bayar a 2023, shi ne na farko a Afirka, kuma na takwas a duniya a jerin 'yan takara.

Ya ci kwallo 26 ya taimakawa Napoli ta lashe Serie A na farko a tarihi, bayan shekara 33.

To sai dai idan bai lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na 2023 ba, zai bi sahun fitattun 'yan wasan nahiyar da ba su samu damar lashe kyautar ba.

BBC ta zakulo muku wasu daga cikin 'yan wasa biyar da suka yi fice amma ba su taba cin kyautar ba.

Jay-Jay Okocha (Najeriya)

Kaka uku ana sa sunan tsohon dan kwallon tawagar Super Eagles cikin masu takara, wanda ake cewa babu kamarsa a fannin yanka da murza leda a nahiyar.

Yana cikin matasan Najeriya da suka lashe kofin Afirka a 1994 da lambar yabo ta zinare a Olympic a 1996, bayan doke Argentina da Brazil.

A shekarar 1998 Okocha ya taka rawar gani fiye da kowacce a gasar kofin duniya a Faransa, duk da an cire SuperEagles a matakin zagaye na 'yan 16.

Okocha ya yi na biyu a kyautar gwarzon dan kwallon Afirka, bayan da dan wasan Morocco, Mustapha Hadji ya zama zakara da tazarar maki biyu.

A shekarar 2003 da 2004 ya kare a mataki na uku, bayan da dan wasan Kamaru, Samuel Eto'o ya lashe kyautar, duk da cewar Okocha ya yi kan--kan--kan da tsohon dan wasan Barcelona a yawan cin kwallaye a Afcon 2004.

A shekarar 2013 tsohon dan wasan Chelsea, John Obi Mikel ya zama na biyu, sai tsohon dan kwallon Everton, Daniel Amokachi ya yi na uku a 1995 da kuma 1996.

Michael Essien (Ghana)

Wani fitatcen dan wasan shi ne Michael Essien dan kwallon tawagar Ghana, wanda shima bai taba lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka ba.

Essien ya lashe kofin gasar Faransa karo biyu a jere a Lyon, kuma shi ne aka zaba fitatcen dan kwallo a Ligue 1 a 2005, daga nan ya koma Chelsea da taka leda kan mafi tsada daga Afirka kan £24.4 million.

Dan kwallon tawagar Ghana ya zama fitatcen dan wasan Chelsea tsawon lokaci a Stamford Bridge, wanda ya taimaka kungiyar ta dauki Premier League biyu da FA Cup hudu da Champions League a 2012.

Ya shiga cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon Afirka a kowacce shekara tun daga 2005 zuwa 2009, wanda ya yi na biyu a 2007, bayan da dan kwallon Mali, Frederic Kanoute ya lashe kyautar.

Wani dan wasan Ghana, Asamoah Gyan yana cikin 'yan wasa fitattu da bai taba lashe kyautar ba, wanda ya yi na biyu a 2010 a kyautar da Eto'o ya zama zakara.

Yayin da tsohon mai tsaron bayan, tawagar Ghana da Bayern Munich, Samuel Kuffour ya yi na biyu a shekarar 1999 da kuma 2001.

Mohamed Aboutrika (Masar)

Masar ta taka rawar gani a kwallon nahiyar Afirka tsakanin 2006 zuwa 2010, kuma dan wasan da yake jan ragamar tawagar a kwazo shi ne Mohamed Aboutrika.

Aboutrika ya karbi kyautar fitatcen dan wasa a tsakanin kungiyoyin da ke taka leda a Afirka karo hudu da saka shi cikin 'yan kwallo Afirka 11 sau hudu.

Wanda bai yadda ya je wata kasa buga wasa ba, ya yi na biyu a 2008, bayan da Emmanuel Adebayor ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka.

Shima dan wasan Masar, Hossam Hassan bai taba lashe kyautar ba a sama da shekara 20 da ya taka leda, wanda ya dauki kofin Afirka uku da zama kan gaba a cin kwallaye a gasar Afcon a 1998.

Benni McCarthy (South Africa)

Benni McCarthy shi ne ya yi na daya a cin kwallaye a gasar Portugal a 2004 da daukar Uefa Champions League da Intercontinental Cup da Porto.

Haka kuma ya yi kan-kan-kan a cin kwallaye a gasar Afirka a 1998 mai bakwai a raga tare da Hassan

Kwallon da ya buga tare da Shaun Bartlett a Bafana Bafana sun sa tawagar Afirka ta Kudu ta yi fice a lokacin, wadda ta buga gasar kofin duniya 1998 da kuma 2002.

To sai dai McCarthy baya cikin 'yan kwallon Afirka ta Kudu da suka lashe kofin Afirka a 1996 a kasar da karbar bakuncin kofin duniya a 2010.

Duk da lashe kofi a gasar Netherlands da ta Portugal, McCarthy bai taba shiga cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon kafar Afirka ba na shekara.

Shima Christopher Katongo bai lashe kyautar ba a 2012, bayan da dan wasan tawagar Zambia ya ci kofin Afirka.

Sai dai ya samu kaso 40 cikin dari a 2012 a takarar gwarzon dan wasan Afirka da BBC ke karramawa.

Seydou Keita (Mali)

Seydou Keita ya taka rawar gani a kungiyar Barcelona a lokacin Pep Guardiola, wadanda suka lashe La Liga uku a jere tsakanin 2009 zuwa 2011.

Shi ne na farko da ya fara taka leda a Barcelona dan kasar Mali, tun bayan da ya koma Sifaniya da taka leda daga Sevilla a 2008.

Ya lashe Champions League da Uefa Super Cup da Club World Cup a Barcelona a 2009 da kuma 2011, yana cikin 'yan wasan Afirka 11 na hukumar kwallon kafar Afirka.

Keita ya yi na biyu a kyautar da Yaya Toure ya zama zakara a 2011, ya taimakawa Mali ta yi ta uku a gasar cin kofin Afirka a 2012 da kuma a 2012.

Kalidou Koulibaly wani dan kwallon ne da bai lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ba, wanda bai samu shiga takara a 2020 da 2021 ba, sakamakon bullar cutar korona.

Yanzu yana taka leda a Saudi Arabia a kungiyar Al-Hilal, shi ne kyaftin din Senegal da ta lashe kofin Afirka a karon farko a tarihi a Kamaru.

Source: BBC