0
MenuAfrica
BBC

Florentino Perez zai ci gaba da shugabantar Real Madrid zuwa 2025

Tue, 13 Apr 2021 Source: bbc.com

Ranar Talata Real Madrid ta gudanar da taron daraktocinta, inda ta tabbatar da Florentino Perez a matakin zai ci gaba da jan ragama zuwa 2025.

Mutan uku ne mataimakansa da suka hada da Fernando Fernandez Tapias da Eduardo Fernandez de Blas da kuma Pedro Lopez Jimenez.

Yayin da Enrique Sanchez Gonzalez ke matsayin maga takardan Real Madrid.

Perez ya fara jagoranta Real a Yulin 2000, kawo yanzu ya lashe kofi 47 a karkashin jagorancinsa ciki har da 26 a kwallon kafa da 21 a kwallon kwandon kungiyar.

Kofin da ya ja ragama aka ci a kwallon kafa sun hada da European Cup biyar da Club World Cups biyar da European Super Cups hudu da La Liga 5 da Copa del Rey biyu da kuma Spanish Super Cups biyar.

A fannin kwallon kwandon kungiyar Real kuwa ya jagoranci lashe European Cup biyu da Intercontinental Cup 1 da Leagues 6 da Copa del Rey 6 daSpanish Super Cup shida.

Florentino Perez na fuskantar karo na shida a matakin shugaban Real Madrid da wa'adin zai kare a 2025.

Source: bbc.com