BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Florenzi na fuskantar bincike kan harkar caca

34097817 Alessandro Florenzi

Thu, 16 Nov 2023 Source: BBC

Ana binciken mai tsaron bayan AC Milan Alessandro Florenzi bisa zargin yin caca ba bisa ƙa'ida ba, makonni bayan da aka dakatar da Sandro Tonali da Nicolo Fagioli.

Bayan hukuncin da ta yanke kan Tonali da Fagioli, binciken ya ci gaba da gudana a bayan fage kuma hukumomi sun gaya wa Florenzi cewa ana kan bincikensa.

Ana sa ran Florenzi zai gana da mai shigar da ƙara na Italiya nan da kwanaki masu zuwa domin tattaunawa kan lamarin.

Ya kasance ɗan wasa mai muhimmanci a tawagar Milan kuma ya fara wasanni biyar na Seria A wannan kakar, yayin da ya shiga wasan daga benci a wasu wasanni biyar.

Yana fuskantar tashin hankali kan sakamakon binciken yayin da Milan za ta dawo taka leda a ranar 25 ga watan Nuwamba bayan hutun wasannin ƙasa da ƙasa inda za ta kara da Fiorentina.

Source: BBC